Kwankwaso Ya Yi Magana kan Rashin Tsaro, Ya Ba 'Yan Siyasa Shawara

Kwankwaso Ya Yi Magana kan Rashin Tsaro, Ya Ba 'Yan Siyasa Shawara

  • Jigo a jam'iyyar APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da aka fama da ita a ƙasar nan
  • Kwankwaso ya yi gargaɗi kan sanya siyasa a cikin matsalar rashin wanda ya bayyana a matsayin abin da zai kawo cikas ga ƙoƙarin da gwamnati take yi
  • Ya yaba da matakin da ƙaramin tsaro, Bello Matawalle, ya ɗauka na komawa Sokoto domin yaƙar ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya gargaɗi ƴan Najeriya da su daina siyasantar da al’amuran tsaro.

Kwankwaso ya bayyana cewa siyasantar da al’amuran tsaro na kawo cikas ga ci gaban yaƙi da rashin tsaro da gwamnatin tarayya ke yi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bugi kirji kan zaben 2027, ya fadi abin da zai faru

Kwankwaso ya ba 'yan siyasa shawara
Kwankwaso ya bukaci a daina sa siyasa cikin matsalar rashin tsaro Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ce ya bayar da wannan shawarar ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya yabawa Matawalle

Kwankwaso ya yaba da matakin da ƙaramin minista tsaro ya ɗauka na komawa Sokoto domin yaƙar ƴan bindiga.

Jigon na APC ya kuma yaba da ƙoƙarin Matawalle, wanda ya sanar da bayar da tukuicin N20m ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kamo ƴan bindiga, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Me ya ce kan rashin tsaro?

"Da farko mutane suna sukar ma'aikatar tsaro saboda ta ƙi ɗaukar matakai, amma yanzu da aka ɗauki matakan yaƙi da ƴan ta'addan, waɗannan mutanen sun dawo suna caccakar ma'aikatar. Wannan munafurci ne."
"Waɗanda suke yin hakan suna cin gajiyar ta'addancin da yake kashe mana mutane, shiyasa suka mayar da lamarin ya zama siyasa."

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi dalilin 'yan bindiga na daukar makamai

"Ƴan ta'addan nan na kashe mutane a kullum kuma lamarin ya taɓarɓare, yanzu ma'aikatar ta ɗauki matakai ta yadda har an kashe ƴan ta'adda 80, meyasa mutum mai hankali zai fito ya soki hakan?"

- Musa Iliyasu Kwankwaso

Ya kuma ƙara da cewa masu sukar gwamnatin tarayya kan matakan da ta ɗauka a fannin tsaro suna son ɓata sunan shugaban ƙasa ne kawai saboda tunanin 2027 wanda ba domin ƙasar nan suke yi ba.

Kwankwaso ya magantu kan shirin haɗaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam'iyyar APC a jihar Kano ya yi magana kan hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce su dukansu ɓata lokacinsu suke yi wurin haɗaka saboda zaɓen 2027 mai zuwa domin ba za su yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng