"Na Rasa Uwa": Jonathan Ya Fadi Alherin da Marigayiya Hajiya Dada Ta Yi Masa

"Na Rasa Uwa": Jonathan Ya Fadi Alherin da Marigayiya Hajiya Dada Ta Yi Masa

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya nuna alhini bayan rasuwar Hajiya Dada a jihar Katsina
  • Jonathan ya yi ta'azziya inda ya ce tabbas wannar mutuwa shi aka yiwa saboda ya dauke ta kamar uwa
  • Wannan na zuwa ne bayan rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'Adua a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi jimamin rasuwar Hajiya Dada a Katsina.

Jonathan ya ce tabbas wannar mutuwa shi aka yi wa saboda ya dauki Hajiya Dada kamar uwa.

Jonathan ya yi ta'azziya game da rasuwar Hajiya Dada a Katsina
Goodluck Jonathan ya nuna alhini bayan rasuwar Hajiya Dada a jihar Katsina. Hoto: Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

Dada: Jonathan ya yi ta'azziya bayan rasuwarta

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a yau Asabar 7 ga watan Satumbar 2024 yayin ziyarar ta'azziya, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

2027: Malamin addini ya ba Jonathan shawara kan tsayawa takara, ya fadi abin da zai faru

Jonathan ya ce marigayiwar ita ta mayar da shi yadda ya ke a yanzu wanda ba zai taba mantawa ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ya ce ya samu labarin rasuwar lokacin da ya ke kan hanyar birnin Kigali ta kasar Rwanda inda ya ce ya dawo Najeriya jiya Juma'a.

Jonathan ya fadi alherin da ta yi masa

"Tabbas abin ya taba ni, danta ne ya dauke ni mataimaki, ba tare da marigayiyar ba da ba a ko san sunana ba."
"Wannan mutuwa kamar mahaifiya ta ce ta rasu saboda yadda na dauke ta uwa a gare ni."
"Labarin rasuwarta tabbas ya taba ni, ina kan hanyar zuwa Kigali a ranar Litinin na samu mummunan labarin."

- Goodluck Jonathan

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar marigayiya Hajiya Dada a ranar Litinin 2 ga watan Satumbar 2024 a asibiti da ke jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa bai kamata Goodluck Jonathan ya sake neman takara a 2027 ba'

Hajiya Dada: Bashir Ahmad ya kare Buhari

A wani labarin, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a bangaren sadarwa, Bashir Ahmad ya kare mai gidansa.

Bashir Ahmad ya ce Buhari bai gida Najeriya ne shi yasa bai halarci jana'izar marigayiya Hajiya Dada ba.

Hakan na zuwa ne bayan cece-kuce da ake ta yi na cewa ba a ga Buhari a wurin jana'izar ba da aka gudanar a Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.