Matatar Dangote: NNPCL Ya Yi Magana kan Yiwuwar Farashin Fetur Ya Sauka

Matatar Dangote: NNPCL Ya Yi Magana kan Yiwuwar Farashin Fetur Ya Sauka

  • Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi maganan kan yiwuwar a samu sauki tsadar farashin fetur biyo bayan fara aikin da matatar Dangote ta yi
  • Kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa fara samar da man fetur a matatar Dangote ba shi ba ne zai sanya farashinsa ya yi sauƙi ba a ƙasar nan
  • A ranar 15 ga watan Satumban 2024 ne ake sa ran kamfanin NNPCL zai fara jigilar man fetur daga matatar Dangote wacce ke a birnin Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi magana kan raguwar farashin man fetur sakamakon fara aikin matatar Dangote.

Kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa cewa fara jigilar man fetur daga matatar Dangote ba shi ba ne yake nuna za a samun raguwar farashin man fetur ɗin ba.

Kara karanta wannan

Dangote: NNPC ya ba matatun Najeriya ikon sayar da fetur kai tsaye ga 'yan kasuwa

NNPCL ya magantu kan farashin fetur
NNPCL ya ce babu tabbaci matatar Dangote za ta sa farashin fetur ya ragu Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Me NNPCL ya ce kan farashin fetur?

A wata sanarwa a shafin X na kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa fara tace man fetur a matatar Dangote ba shi ba ne yake nuna za a samu raguwar farashinsa a kasuwa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olufemi Soneye wanda shi ne babban jami'in ɓangaren sadarwa na NNPCL ya bayyana cewa farashin man fetur yana tafiya ne daidai da daidai kan yadda yake a kasuwannin duniya.

Soneye ya bayyana cewa tace man fetur a cikin gida ba shi ba ne dalilin da zai sanya a samu raguwar farashinsa ba.

A ranar 15 ga watan Satumba ne dai ake sa ran kamfanin mai na NNPCL zai fara jigilar man fetur daga matatar Dangote.

Karanta wasu labaran kan NNPCL

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Dangote ba zai siyar da mai kasa da farashin kamfanin NNPCL ba'

Dangote zai iya ba ƴan kasuwa fetur - NNPCL

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin mai na Najeriya (NNPC Ltd) ya bayyana cewa Dangote da sauran matatun man Najeriya na da ‘yancin sayar da fetur kai tsaye ga ƴan kasuwa.

NNPC ya yi martani ne ga ikirarin da kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi a baya-bayan nan da ke nuna cewa kamfanin na adawa da matatar man Dangote (DRL).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng