Tsadar Mai: Gwamna Ya Dakatar da Bude Duka Makarantun Jiharsa, Ya ba da Shawara

Tsadar Mai: Gwamna Ya Dakatar da Bude Duka Makarantun Jiharsa, Ya ba da Shawara

  • Gwamnatin jihar Edo ta ba da sabuwar sanarwar kan bude makarantun gwamnati da masu zaman kansu
  • Gwamnatin ta umarci dakatar da bude makarantun a ranar 9 ga watan Satumbar 2024 har sai baba ta gani
  • Wannan na zuwa ne bayan kara farashin mai a kasar da aka yi wanda ya jefa al'umma cikin matsi da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamnatin jihar Edo ta dakatar da komawa makarantu da dalibai ke shirin yi a fadin jihar.

Gwamnatin ta dauki matakin ne duba da yadda mutane ke cikin wani hali bayan kara farashin mai.

Gwamna ya dakatar da bude makarantu saboda tsadar mai
Gwamna Godwin Obaseki ya dakatar da komawa makarantu a Edo saboda tsadar mai. Hoto: Godwin Obaseki.
Asali: Facebook

Tsadar mai: Obaseki ya dakatar da bude makarantu

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Sakataren din-din-din a ma'aikatar ilimi, Ojo Akin-Longe shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 7 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

Akin-Longe ya ce an dage shirin dawowa makarantu da aka yi niyya a ranar 9 ga watan Satumbar 2024 har sai baba ta gani, Tribune ta ruwaito.

Sanarwar ta umarci dukan makarantu su kasance a kulle saboda irin kunci da iyaye za su shiga yayin kai 'ya'yansu makaranta.

"Gwamnatin Edo ta sanar da dage bude makarantu da aka yi niyya a ranar 9 ga watan Satumbar 2024 har sai baba ta gani."
"Sanarwar ta bukaci makarantu su kasance a kulle saboda halin da aka shiga bayan kara kudin mai da kuma wahalar da iyaye suke ciki.

- Ojo Akin-Longe

Obaseki ya shawarci al'umma kan tsadar mai

Kara karanta wannan

Dattawan Yarabawa sun yi adawa da karin kudin fetur, sun aika sako ga Tinubu

Gwamnatin daga bisani ta bukaci iyaye da kuma da zirga-zirgar ƴaƴansu saboda halin da ake ciki bayan kara farashin mai da abin da iya jawowa.

Matakin zai shafi dukan makarantu da suka hada da na gwamanti da kuma masu zaman kansu gaba daya a jihar.

Tsadar mai: Gwamnatin Kwara ta tallafawa al'umma

Kun ji cewa yayin da ake cikin mawuyacin hali bayan kara farashin mai a Najeriya, Gwamnatin jihar Kwara ta agazawa al'ummarta.

Gwamnatin ta ba da umarnin samar da bas musamman a cikin birni domin zirga-zirgar jama'a wurare daban-daban.

Gwamnatin jihar ta roki al'umma da masu ababan hawa da su kara hakuri ana neman hanyoyin magance matsalolin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.