'Abin da Ya Sa Dangote ba Zai Siyar da Mai Kasa da Farashin Kamfanin NNPCL ba'
- Wani masanin harkokin mai a Najeriya, Henry Adigun ya yi fashin baki kan farashin da matatar Dangote za ta tsaida
- Adigun ya ce ba zai taba yiwuwa Dangote ya siyar a farashi kasa da na kamfanin NNPCL ba saboda ana lissafi da dala ne
- Mai fashin bakin ya kuma ce man Dangote shi ne mafi kyau a duniya domin haka duk abin da yake da kyau zai yi tsada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wani masanin harkokin man fetur a Najeriya ya yi magana kan farashin mai a matatar Aliko Dangote.
Mr. Henry Adigun ya ce zai yi wahala Dangote ya siyar da mai kasa da farashin kamfanin NNPCL a yanzu.
Masani ya magantu kan farashin man Dangote
Adigun ya bayyana haka ne a yau Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024 yayin hira da Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masanin ya ce yawan amfani da dala a harkokin gudanar da matatar shi ne babban dalilin da ya sa man zai yi tsada.
Ya ce man da matatar Dangote ke fitarwa shi ne mafi kyau a duniya wanda dole zai saka ya yi tsada.
'Man Dangote shi ne mafi kyau' - Masani
"Ina cigaba da fadawa mutane, Dangote ya dauki bashi a dala ba Naira ba, kuma zai cigaba da biyan bashin a dala."
"Ba zai taba siyarwa kasa da N850 na NNPCL ba kamar yadda ake zato saboda akwai kudi da ake kashewa na shiga da wani kaso na mai."
- Henry Adigun
Adigun ya ce Dangote yana samun 40% ne na danyen mai daga NNPCL sannan ya siyo sauran daga Amurka saboda ba za a yi amfani da kala daya ba.
Yadda aka illata Otedola da Dangote
A wani labarin, kun ji cewa Femi Otedola ya koka kan yadda gwamnatin marigayi Umaru Yar'Adua ta dakile shi da Aliko Dangote.
Odetola ya bayyana cewa sun shirya mallakar matatun mai a Kaduna da Port Harcourt amma shugaba Yar'Adua ya rusa tsarin.
Ya ce sun kulla yarjejeniya na siyan hannun jari a matatun biyu a mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kafin ya sauka.
Asali: Legit.ng