An Soki Barau Jibrin kan Karbar Mutane zuwa APC alhali Ana Kukan Kuncin Rayuwa
- Dare da rana labarin da ake samu shi ne Barau I. Jibrin yana daukewa Kwankwasiyya da NNPP mabiya zuwa APC
- Wasu sun fara zargin mataimakin shugaban majalisar dattawan da biyewa siyasa a lokacin da mulki ne gabansa
- A gefe guda kuwa, akwai masoya Kwankwasiyya da suka fara tsorata da abin da yake faruwa a jam’iyyar NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - A ‘yan kwana biyun nan, kusan kullum sai an ji labarin Sanata Barau I. Jibrin ya karbi wasu da suka shigo jam’iyyar APC.
Mafi yawan wadanda ake yi wa wankan shigowa APC mai mulkin kasa da rinjaye a majalisar tarayya ‘yan Kwankwasiyya ne.
Sanata Barau Jibrin ya gamu da suka
Wata ma’abociyar dandalin sada zumunta na X ta fusata da yadda aka fi jin Sanata Barau I. Jibrin ya maida hankalin kan siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adda Fadi ta caccaki mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar, ta ke mamakin ko bai da wani muhimmin aiki ne.
Barau ya manta da matsalolin Arewa?
Wannan baiwar Allah ta bayyana haka ne duba da matsayinsa a majalisar tarayya a daidai lokacin da ake ta fama da kasha-kashe.
Bayan matsalar rashin tsaro a yankin da Barau ya fito na a Arewa, ana cikin kuncin rayuwa da kuma wahala saboda tsadar man fetur.
Abin da ta ke so shi ne a sanar da shugaban kasa halin da mutanen Arewa suke ciki.
“Wai ba ka da aiki ne a ofishinka sai karban mutane? Baka san ana kashe mutane a Arewa ba ne? Ko baka san halin da Nigeria ke ciki ba?
Yau wata biyu muna layin mai, dukkanku ku na can baku da amfani…”
- Adda Fadi
Barau yana nakasa Kwankwasiyya
A game da abubuwan da ke faruwa na sauya-shekar ‘Yan Kwankwasiyya, an ji Dr. Fahad Danladi a shafinsa na Facebook yana korafi.
Masoyin Kwankwasiyyar ya ce bai kamata NNPP mai mulki ta rika rasa mabiya, ya ce akwai matsala daga masu mulki da jagoransu.
"Mu na da gwamnati a Kano, amma magoya baya na ficewa. A ina a ka haihu a ragaya?
"Akwai matsala daga jagora da kuma gwamna. Zan rubuta mu su ƙorafi da shawarwari na a rubuce, na aika mu su a sirrance."
- Fahad Ibrahim Danladi
Abba ya sharewa tsoho hawaye
Kwanakin bayan wani tsoho ya fito neman taimako, an ji labari Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ba shi kyautar Naira miliyan daya.
An ce gwamnan jihar Kano ya yi umarni a nemo masa gida mai kyau a Unguwar da yake zama kuma ya hada masa da abinci.
Asali: Legit.ng