Malamin Musulunci Ya Yi Bakar Addu’a ga Masu Mulki saboda Karin Kudin Man Fetur
- Sheikh Kabir Bashir Abdulhameed ya yi korafi da ya ji labarin fetur ya tashi tun daga gidajen man NNPCL
- Malamin addinin ya yi addu’a Allah SWT yayi maganin mugayen masu mulki a Najeriya ta yadda ya ga dama
- Kabir Bashir Abdulhameed ya na ganin dole sai al’umma sun tashi tsaye sannan za a samu sauki a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Kabir Bashir Abdulhamid yana cikin malaman addinin da suka fusata da jin cewa litar man fetur ta kara tsada a Najeriya.
Malaman musulunci da na kirista da-dama sun yi tarayya wajen yin Allah-wadai da jin fetur ya kara kudi a gidajen man NNPCL.
Tashin fetur ya fusata Sheikh Kabir Abdulhamid
A shafinsa na Facebook, a tsakiyar makon nan Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid ya yi mummunar addu’a ga masu mulkin kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin musuluncin ya roki Ubangiji Madaukakin Sarki ya yi maganin mugayen shugabannin Najeriya da suke zaluntar talaka.
Kabir Bashir Abdulhamid ya koka ganin yadda jama’a suke rayuwar kunci duk da irin dinbin arzikin da Allah SWT ya yi wa kasar.
Malami ya yi addu'a kan tsadar man fetur
“Allah mu ke roko da mafi kyawawan sunayansa da Sifofinsa madaukaka da ya yi mana maganin wadannan lalatattun shugabanni, ya haramtamusu jin dadi duniya da lahira,
"Mu da arzikin kasarmu amma azzalumai suna ganamana azaba akansa.
"Wajibi talaka ya tashi ya nemi yancinsa kafin su karasa tarwatsa kasar kowa ya kama gabansa."
- Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid
A maganar da ya yi a shafinsa, malamin ya yi kira ga jama’a su tashi su nemawa kansu ‘yanci kafin a gama raga-raga da kasar.
Fetur ya tashi, albashi bai motsa ba
Bayan nan kuma an ji matashin malamin ya na zancen albashi, ya soki gwamnati saboda kin soma biyan albashin akalla N70, 000.
A lokacin da aka yi ta dogon turanci kafin a yarda da biyan N70, 000, da aka tashi kara kudin fetur, shehin ya ce rana daya da aka yi.
Malamin ya ba da labarin yadda suka samu fetur da kyar a kan hanyar Kano, shi ma sai da Sheikh Alkali Zariya ya nema masu alfarma.
Masu mulki da suka bar gwamnarin Tinubu
Kwanaki rahoto ya zo cewa akwai manyan jami’an da suka ajiye mukaminsu, suka bar aiki a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Wanda ya fara bin wannan layi da aka canza gwamnati shi ne tsohon shugaban NUC daga baya ne shugaban NIA ya yi koyi da shi.
Asali: Legit.ng