Tinubu Ya Fadi Nasarorin da Ya Samu a China, Ya Bayyana Amfanin Kara Kudin Mai

Tinubu Ya Fadi Nasarorin da Ya Samu a China, Ya Bayyana Amfanin Kara Kudin Mai

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci yan Najeriya mazauna China da su tabbatar da sun wakilci kasarsu a ketare
  • Tinubu ya fadi irin nasarorin da ya samu yayin ziyarar kwanaki da ya yi kasar China inda ya sake rokon yan Najeriya
  • Shugaban ya bayyana amfanin karin kudin mai inda ya ce ba tare da samun kudin shiga ba, babu damar yin ayyukan alheri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kasar China - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana irin nasarorin da ya samu yayin ziyararsa a kasar China.

Tinubu ya ce sun sanya hannun a yarjejeniya da Shugaba Xi Jinping wurin inganta tattalin arziki da sauran lamura.

Tinubu ya yi magana kan karin farashin man fetur
Bola Tinubu ya bukaci karin hakuri kan matakan da ya ke dauka. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya kammala ziyara a China

Kara karanta wannan

'Ana yunwa,' Malamin addini ya tsage gaskiya a gaban jiga jigan APC a Abuja

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafin Facebook.

Tinubu ya fadi haka ne yayin ganawa da yan Najeriya da ke zama a kasar a otal na China World Hotel.

Shugaban ya shawarci yan Najeriya mazauna China da su kasance mutanen kirki domin daga darajar kasarsu.

Ya ce Najeriya tana kan hanyar samun cigaba saboda daukar matakai masu tsauri da ake yi musamman karin kudin fetur da kuke ji.

Tinubu ya fadi hanyar samun cigaba

"Muna daukar wasu tsauraran matakai domin kawo cigaba, za ku iya samun labari a gida a kwanakin nan kan karin kudin fetur."
"Abin da ke faruwa shi ne idan ba mu dauki tsauraran matakai ba, babu yadda za a samu cigaba kamar yadda kuke da shi a nan China."

Kara karanta wannan

'Fir'aunanci ne,' Malamin addini ya dura kan gwamnatin Tinubu a kan tashin man fetur

- Bola Tinubu

Tinubu ya ce yana da tabbaci kan mukarrabansa inda ya ce ya samu abokan aiki nagari wurin kawo sauyi a kasar.

Tinubu ya yi magana kan karancin mai

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa nan da karshen makon nan fetur zai wadata a fadin kasar, saboda haka jama'a su kwantar da hankula.

Karamin ministan man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana hakan bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Heineken Lokpobiri ya ce 'yan Najeriya su sani cewa gwamnati ba ta kayyade farashi ba, kuma wadatar fetur zai sa farashinsa ya daidaita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.