Gwamnatin Tinubu Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Faɗi Gaskiya kan Shekarun Rubuta WAEC da NECO

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Faɗi Gaskiya kan Shekarun Rubuta WAEC da NECO

  • Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan batun mafi karancin shekarun zana jarabawar fita sakandire WAEC, NECO da NABTEB
  • Karamin ministan ilimi, Dr Tanko Sununu ya ce jarabawar share fagen shiga jami'o'i ce aka sanya wa dokar cika shekara 18
  • Wannan bayani na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun yi ikirarin gwamnati ta yanke shekara 18 a matsayin shekarun zana jarrabawar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagoranci Bola Ahmed Tinubu ta yi ƙarin haske kan batun mafi ƙarancin shekarun zana jarabawar gama sakandire a Najeriya.

Rahotannin da ke yawo sun yi iƙirarin cewa gwamnatin ta yanke cewa dole sai ɗalibi ya kai shekaru 18 gabanin a ba shi damar zana jarabawar WAEC da NECO.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya ba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya yiwa ministocinsa

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta musanta raɗe-raɗin kayyade shekarun zama WAEC da NECO Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya ta fayyace batun WAEC/NECO

Sai dai gwamnatin Tinubu ta musanta raɗe-raɗin inda ta ce jarabawar JAMB ta share fagen shiga jami'o'i ce ta sanyawa mafi ƙarancin shekaru 18, rahoton Punch.

Leadership ta ce ƙaramin ministan ilimi, Dr. Tanko Sununu ne ya bayyana hakan yayin zantawa da ƴan jarida ranar Jumu'a a Abuja.

Ya ce gwamnati dai ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi karancin shekarun zana jarabawar UTME wacce hukumar JAMB ke shiryawa.

UTME: Matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka

"Game da wannan batun, mun riga mun yi bayani ba sau ɗaya ba, babu wurin da ministan ilimi, Tahir Mamman ko ƙaramin minista suka yi maganar ƙarancin shekarun zama WAEC, NECO ko NABTEB."
"Jama'a sun tsinci wasu kalamai daga jawabin minista, suka masa gurguwar fassara cewa an ƙayyade shekarun WAEC da NECO.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya shiga matsala bayan ya yi wa wasu gwamnoni barazana

"Abin da muka faɗa a baya shi ne shekarun shiga jami'a da jarabawar UTME, mun yi bayani mai gamsarwa kuma matakin ya yi daidai da tsarin ilimin ƙasar nan."

- Tanko Sanunu.

Gwamnatin tarayya ta waiwayo masu POS

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta hannun hukumar CAC ta ce wa'adin da ta ba masu POS su yi rijista ya cika a ranar 5 ga watan Satumba, 2024.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Jumu'a, CAC ta ce ba za a ƙyale waɗanda suka yi wa umarninta kunnen ƙashi ba, za ta ɗauki mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262