Kotu Ta Ingiza Keyar Hadimin Tambuwal Kurkuku kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
- Kotun majistare da ke zamanta a Sakkwato ta tura Shafi’u Umar Tureta, hadimin Aminu Waziri Tambuwal gidan yari
- Ana zargin Tureta da cin zarafin gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu da matarsa, Hajiya Fatima Aliyu a shafukan sada zumunta
- Shafi'u Umar Tureta ya wallafa bidiyon Hajiya Fatima ta na watsa kudi yayin bikin zagayowar ranar haihuwarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Kotun majistare da ke zamanta a Sakkwato ta tura Shafi’u Umar Tureta gidan yari bisa zargin cin zarafin gwamnan jiharsa, Ahmed Aliyu.
Haka kuma ana zargin Tureta,wanda hadimin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne da wallafa bidiyo bidiyon matar gwamnan ta na watsa kudi a murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana zargin Shafi'u Tureta da yada karya da cin zarafin gwamnan Ahmad Aliyu da matarsa, Fatima Ahmed Aliyu.
An yi zargin cin zarafin gwamnan Sakkwato
Peoples Gazette ta wallafa cewa ana zargin hadimin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal da cin zarafin gwamnan mai-ci, Ahmed Aliyu.
Takardar na nuna sakamakon jarrabawar gwamna Ahmed da ke nuna cewa ya fadi SSCE warwas, kuma da kyar ya ke hada kalaman turanci domin magana da yaren.
An rufe tsohon hadimin gwamnan Sakkwato
Bayan sauraron shari'ar da karantawa wanda ake zargi laifinsa ne Tureta ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.
Duk da lauyansa Barista Al'Mustapha Abubakar ya nemi beli, amma Mai Shari'a Fatima Hassan ta aika da shi gidan gyaran hali zuwa 18 Satumba, 2024.
Sakkwato: An kama tsohon hadimin gwamna
A baya kun ji cewa an aika tsohon hadimin gwamna Tambuwal, Shafi'u Umar Tureta gidan yari bisa zargin wallafa bidiyo da ke nuna gwamna Ahmed Aliyu na kokarin turanci.
Ana zargin Tureta da yada karya , wanda ya zama cin zarafin gwamna mai ci da matarsa ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta inda ya wallafa bidiyo da takarda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng