‘Fir’aunanci ne,’ Malamin Addini Ya Dura kan Gwamnatin Tinubu a kan Tashin Man Fetur
- Shahararren malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Muhammad Adamu Dokoro ya yi zazzafan martani kan karin kudin mai
- Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya ce Fir'aunanci da masu rike da madafun iko ke yi a tarayyar Najeriya ya wuce gona da iri a yau
- Legit ta tattauna da wani magidanci, Muhammad Babayo kan jin halin da ya samu kansa sakamakon karin kudin mai da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Adamu Dokoro ya nuna damuwa kan kara kuɗin man fetur.
Sheikh Adamu Dokoro ya ce masu mulki a Najeriya ba su nuna tausayi ga talakawa kwata kwata.
Legit ta tatttaro abin da malamin ya fada ne a cikin wani bidiyo da Tahir Abubakar ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Fir'aunanci ya yi yawa' Inji Sheikh Dokoro
Sheikh Adamu Dokoro ya ce sam babu alamar hankali a wayi gari da mugun karin kuɗin man fetur babu zato babu tsammani.
Shehin malamin ya koka kan haka inda ya ce Fir'aunanci da shugabanni suke yi a Najeriya ya yi yawa matuka.
Tashin kudin fetur zai yamutsa Najeriya
Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya ce mutane suna fama da rashin kuɗi da rashin ayyuka kuma aka kara musu wahala.
A kan haka malamin ya ce kamar shugabannin so suke kasar ta yamutse ta inda abubuwa za su lalace a rasa zaman lafiya.
"Gwara a mutu a huta" Inji Sheikh Dokoro
Sheikh Adamu Dokoro ya ce da rayuwar da ake yi a Najeriya gwara a mutu a koma ga Allah ko za a samu sauki.
Malamin ya ce ga yan bindiga an gaza gamawa da su kuma an juyo ana so a kashe talakawa a tsaye.
Legit ta tattauna da Muhammad Babayo
Wani magidanci mai mata biyu, Muhammad Babayo ya zantawa Legit cewa ya shiga halin da bai taba samun kansa a ciki ba saboda tsadar rayuwa.
Muhammad Babayo ya ce kudin da yake samu ba su isan shi bukatun yau da kullum, mafi yawa suna tafiya ne a harkar zirga zirga.
Ya kuma yi kira ga gwamnati kan ta saurari abin da Malam Dokoro ya fada mata domin tausayawa talakawa.
An bukaci rage kudin man fetur
A wani rahoton, kun ji cewa karin kudin man fetur na cigaba da jawo suka ga gwamnati musamman daga talakawa da jam'iyyun adawa.
'Yan majalisun tarayya sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da farashin man fetur yadda yake domin saukakawa al'ummar Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng