Dada: Sanusi II Ya Dura a Katsina, Ya Fadi Abin da Yar’Adua Ya Yi Masa a 2009
- Yayin da ake jimamin rasuwar mahaifyar Umaru Musa Yar'Adua, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya je ta'aziyya
- Dazu Mai martaban ya isa jihar Katsina, ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayiyar inda ya ce tabbas an yi babban rashin uwa
- Sanusi II ya kai ziyara fadar Sarkin Katsina, Dr. Andulmuminu Kabir Usman inda ya bayyana abin da Yar'Adua ya yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara jihar Katsina domin gaisuwar rasuwar Hajiya Dada.
Sarkin ya nuna damuwa kan rashin dattijuwar da ita ce mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Malam Umaru Musa Yar'Adua.
Sanusi II ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifyar Yar'Adua
Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da @masarautarkano ta wallafa a shafin X a yau Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Sarki Sanusi II ya jagoranci addu'o'i ga marigayiyar tare da yi mata fatan samun rahama.
Hakan na zuwa ne bayan rasuwar mahaifiyar marigayi Umaru Musa Yar'Adua a ranar Litinin 2 ga watan Satumbar 2024.
Sanusi II ya fadi halaccin Yar'Aua
"Muna jajantawa masarauta da gwamanti da al'ummar Katsina gaba daya kan wannan rashi da aka yi na Hajiya Dada."
"Kamar yadda Mai Martaba ya sani tsohon shugaban kasa, Mallam Umaru Musa Yar Adua shi ya nada mu gwamnan babban banki."
"Kuma kullum muna fada kafin ya bamu wannan mukami bai sanmu ba ba mu san shi ba, kuma ba nema muka yi ba wanda wani abu ne mawuyaci."
- Muhammadu Sanusi II
Daga bisani, Sanusi II ya gabatar da addu'o'i inda ya yi addu'ar ubangiji ya yi mata rahama ya sanya ta gidan aljanna.
Sanusi II ya yi ta'aziyya ga Sarkin Ningi
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yabawa marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya kan halayensa.
Muhammadu Sanusi II ya ce marigayin na daya daga cikin sarakuna da suka nuna damuwa lokacin da ya shiga matsala a jihar Kano.
Asali: Legit.ng