Gwamnatin Tinubu Ta Taso Masu POS a Gaba, Za a Fara Kulle Masu Shaguna

Gwamnatin Tinubu Ta Taso Masu POS a Gaba, Za a Fara Kulle Masu Shaguna

  • Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar CAC ta ce wa'adin da ta ba masu POS su yi rijista ya cika a ranar 5 ga watan Satumba, 2024
  • A wata sanarwa da ta fitar ranar Jumu'a, CAC ta ce ba za a ƙyale waɗanda suka yi wa umarninta kunnen ƙashi ba, za ta ɗauki mataki
  • Wannan dai na zuwa ne bayan ƙungiyar masu POS ta kai ƙara gaban kotu, tana ƙalubalantar tilascin yin rijistar CAC da aka kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar kula da harkokin kasuwanci CAC ta bayyana cewa za ta fara ɗaukar matakai kan masu sana'ar PoS bayan wa'adin rijista ya cika.

CAC ta sanar da cewa za ta ɗauki matakai masu tsauri ciki har da rufe wuraren sana'ar POS na waɗanda suka yi kunnen uwar shegu da umarnin rijista.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa a wani harin ta'addanci a Katsina

Masu sana'ar POS.
CAC ta shirya sa kafar wando ɗaya da masu POS da ba su yi rijista ba Hoto: Andrew
Asali: Getty Images

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafa shafinta na manhajar X ranar Jumu'a, 6 ga watan Satumba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin waɗanda suka yi fatali da wa'adin da aka ba su na rijista suna da hannu a wasu haramtattaun harkoki da ba su son a sani.

Masu POS sun kai ƙarar CAC a kotu

Wannan dai na zuwa ne yayin da masu sana'o'in hada-hadar kuɗi POS ƙarƙashin ƙungiyar AMMBAN suka ƙalubalanci matakin CAC na tilasta masu yin rijista.

A cewar ƙungiyar, matakin CAC na matsawa ƴaƴanta dole sai sun yi rijsita da ita ya saɓawa doka.

Idan ba ku manta ba a watanni biyu da suka wuce, CAC ta umarci masu POS a faɗin Najeriya su rijista da hukumar kafin ranar 5 ga watan Satumba, 2024.

CAC ta shirya ɗaukar mataki mai tsauri

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya shiga matsala bayan ya yi wa wasu gwamnoni barazana

Amma da take ƙarin haske bayan wa'adin ya cika, hukumar CAC ta ce:

"Muna tunatar da al'umma musamman masu sana'ar POS cewa wa'adin kwanaki 60 da. aka ba su ranar 7 ga watan Yuli, 2024 su yi rijista da CAC ya cika ranar 5 ga watan Satumba.
"Tuni dai muka fara haɗa kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin ɗaukar matakan da suka dace ciki har da rufe shaguna da shari'a."

Naira ta faɗi a kasuwar gwamnati

A wani rahoton kuma, an ji yayin da ake kuka kan tsadar man fetur, darajar Naira ta ƙara faɗowa ƙasa a kasuwar hada-hadar canji ta gwamnati.

Alkaluman kasuwar NAFEM sun nuna cewa Dalar Amurka ta tashi zuwa N1,639.41 a ranar Alhamis sabanin N1,606 da aka yi ciniki a ranar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262