Karin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince Gwamna Abba Ya Kashe N99bn a Sabon Kasafi

Karin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince Gwamna Abba Ya Kashe N99bn a Sabon Kasafi

  • Majalisar dokokin Kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudi da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika mata
  • Gwamnan ya aika da karin kasafin N99.2bn,wanda majalisa ta ce ta amince da shi saboda muhimman ayyukan da za a yi
  • Da ya ke karin bayani kan kudin, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala ya ce an riga an samu kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika mata.

Kwarya-kwaryar kasafin ya zarce Naira Biliyan 99 domin sanya shi a cikin kasafin kudin shekarar da muke ciki.

Kara karanta wannan

Gwamma ya kafa kwamiti, zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000

Jihar Kano
Majalisar dokokin Kano ta amince da karin kasafin kudin bana Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa wannan na nufin kasafin kudin jihar Kano ya karu daga N437.3bn zuwa N536.5bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta fadi amfanin sabon kasafi

Jaridar Leadership ta wallafa cewa majalisar dokokin Kano ta ce sabon kasafin kudin bana zai taimaka wajen manyan ayyuka, ciki har da sabon albashin ma'aikata.

Gwamnatin tarayya ce dai ta amince da biyan mafi karancin albashi M70,000 ga dukkanin ma'aikatan kasar nan, ciki har da na jihar Kano.

Kano: Majalisa ta fadi inda aka samu kudi

A karin bayanin da Legit ta samu, majalisar dokokin Kano ta ce an riga an samu kudin kasafin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika mata.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Lawan Hussaini Dala ya ce an samu karin kudi daga asusun gwamnatin tarayya da kuma tallafi daga kungiyoyi.

Gwamna ya gabatar wa majalisa sabon kasafi

Kara karanta wannan

Ana kukan kara kudin fetur: Gwamnati ta sanar da shirin kara kudin haraji a Najeriya

A baya mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kwarya-kwaryar kasafin kudi ga majalisar dokoki domin ya samu damar biyan karin albashi.

Shugaban majalisar, Isma'il Falgore ya bayyana cewa babban abin da gwamnati za ta yi da kasafin kudin shi ne biyan karin albashi da mafi karancinsa ya koma N70,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.