N70,000: Gwamnan Arewa Ya yi Albishir kan Fara Biyan Sabon Albashi

N70,000: Gwamnan Arewa Ya yi Albishir kan Fara Biyan Sabon Albashi

  • Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da shirin fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka cimma matsaya da NLC
  • Dikko Umaru Radda ne ya sanar da haka kuma ya ce jihar Katsina za ta kasance a gaba gaba kan maganar ƙarin albashin ma'aikata
  • Sai dai gwamna Radda ya fadi abu daya da yake jira kafin ma'aikatan jihar Katsina su fara karban sabon mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin fara biyan mafi ƙarancin albashi na ₦70,000.

Gwamna Dikko Radda ta yi alkawarin ne yayin da yake magana kan jin ra'ayin al'umma a kan kasafin kudin shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

Radda
Za a fara karin albashi a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da gwamna Radda ya yi ne a cikin wani sako da jami'in yada labaran gwamnatin jihar, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

N70, 000: Gwamna zai kara albashi a Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na ₦70,000 a jihar.

Dikko Umaru Radda ya ce zai zama na gaba gaba wajen biyan sabon albashin domin inganta rayuwar ma'aikata a Katsina.

Yaushe Radda zai kara albashi zuwa ₦70,000?

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce yana jiran gwamnatin tarayya ne ta kammala fitar da tsare tsaren karin albashi kafin ya fara biya.

Radda ya kara da cewa zai cigaba da mayar da hankali kan abubuwan da za su inganta aikin gwamanti a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Gwamma ya kafa kwamiti, zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000

Tsarin daukar ma'aikata a Katsina

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce sun kawo tsari na musamman wanda za rika yin gwaji kafin ɗaukar ma'aikata a Katsina.

Gwamnan ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa waɗanda suke da kwarewa ne aka dauka aiki a jihar.

Zulum zai fara biyan albashi ₦70,000

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Borno ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000, ya kafa kwamitin da zai duba yadda za a aiwatar da dokar.

Sakataren gwamnan jihar Borno, Bukar Tijjani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Maiduguri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng