Ana Kukan Tsadar Fetur, NNPCL Ya Fadi Lokacin da Mai zai Wadata a Kasa

Ana Kukan Tsadar Fetur, NNPCL Ya Fadi Lokacin da Mai zai Wadata a Kasa

  • Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa ya na aiki tukuru domin kawo karshen matsalar fetur a kasar nan
  • Mataimakin shugaban kamfanin, Dapo Segun da ya bayyana haka ya dora laifin karancin fetur kan dalilai da dama
  • NNPCL ya bayyana cewa ya na da kyakkyawar alaka da masu ba shi tataccen fetur, saboda haka babu matsalar shigo da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Yayin da yan kasar nan ke fama da karancin fetur da tsadarsa, kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya ce ya na aiki tukuru domin kawo karshen matsalar.

Mataimakin shugaban kamfanin, Dapo Segun ne ya bayyana haka, inda ya ce NNPCL ba shi da matsalar shigo da fetur cikin kasar nan.

Kara karanta wannan

Dangote: NNPC ya ba matatun Najeriya ikon sayar da fetur kai tsaye ga 'yan kasuwa

NNPCL
Kamfanin NNPC ya ce ya na aikin kawo karshen matsalar fetur Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Jaridar This day ta wallafa cewa Mista Dapo ya ce su na da kyakkyawar alaka da masu sayar masu da fetur, duk da dimbin bashi da ake bin kamfanin.

NNPCL zai cigaba shigo da fetur

Mataimakin shugaban kamfanin NNPC na kasa, Dapo Segun ya bayyana cewa har yanzu kamfanin NNPCL ya na iya shigo da fetur.

Jaridar Punch ta wallafa cewa duk da kamfanin bai fadi lokacin kawo karshen matsalar fetur ba, amma ya ce za a samu saukin matsalar a kwanan nan.

Kamfanin NNPC ya fadi dalilin matsalar fetur

Kamfanin mai na kasa ya dora alhakin karancin fetur da ake fama da shi a kan yadda kasuwar canjin kudi ke tafiya.

Mista Segun ya kara da cewa a halin yanzu, 'yan kasuwa ke juya yadda kasuwar fetur ke gudana a kasar nan, ba wai gwamnati ko NNPCL ba.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

NNPCL da farashin fetur din Dangote

A baya kun ji cewa kamfanin mai na kasa ya ce za a fara sayar da fetur daga matatar man Dangote daga ranar 15 Satumba, 2024 a gidajen mai da ke fadin kasar nan.

A sanarwar da NNPCL ya fitar, kamfanin ya bayyana cewa kasuwa ce za ta kayyade nawa matatar Dangote za ta sayarwa yan kasar nan fetur da aka fara tacewa a Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.