'Yan Bindiga Sun Kai Hari Arewa Maso Yamma, Sun Yi Garkuwa da Mutane 15
- Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace mutane 15 a kauyen Mani da ke a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna
- An rahoto cewa 'yan bindigar sun fara zagaye garin ne da sanyin safiya kafin aukawa mutane, aka sace har mai jego da jariri
- Jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma na ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yau
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Akalla mutane 15 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su a kauyen Mani da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun mamaye garin Mani ne da sanyin safiyar Alhamis, kafin su kai farmaki kan “mata masu shayarwa da matasa”.
'Yan bindiga sun kai hari Kaduna
Mansir Hassan, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna, bai ba da amsa da aka nemi jin ta bakinsa game da harin ba, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma ta na ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a 'yan kwanakin nan.
Zuwa yanzu dai 'yan bindigar da suka sace mutanen Mani ba su tuntubi 'yan uwansu domin maganar kudin fansa ba, lamarin da ya kara jefa mutane a firgici.
"An sace 'yan uwana" - Majiya
Jaridar The Sun ta ruwaito wata majiya ta da nemi a sakaya sunanta ta koka da cewa shida daga cikin 'yan uwanta na cikin wadanda aka sace a harin.
A cewar majiyar:
“An sace mutane 15 daga gidaje uku a kauyen Mani daura da kamfanin taliyar Indomie na Rido da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna da sanyin safiyar yau (Alhamis).
“Yan uwana na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su. Muna cikin tashin hankali yayin da nake isar da wannan sako musamman yadda har yanzu ba mu ji daga gare su ba."
Majiyar ta ce 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutanen ciki har da wata uwa mai shayarwa da ke da yara huɗu, matasa, da kuma jariri.
Kaduna: An kama masu garkuwa da mutane
A wani kokarin na kakkabe 'yan ta'adda tare da dawo da zaman lafiya, rundunar 'yan sandan Kaduna ta yi nasarar cafke wasu mutane 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Mun ruwaito cewa kakakin rundunar jihar, ASP Mansir Hassan ya ce an cafke mutanen a karamar hukumar Lere da wasu garuruwan jihar kuma an kwato makamai da kudi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng