A Ƙarshe Kamfanin NNPC Ya Bayyana Farashin Man Fetur Na Matatar Ɗangote

A Ƙarshe Kamfanin NNPC Ya Bayyana Farashin Man Fetur Na Matatar Ɗangote

  • Kamfanin mai NNPCL ya bayyana cewa man feturin matatar Ɗangote zai fara shiga kasuwa ranar 15 ga watan Satumba, 2024
  • Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce yanayin kasuwa ne zai ƙayyade farashin litar man feturin Ɗangote
  • A farkon makon nan ne Alhaji Ɗangote ya tabbatar da cewa matatarsa ta fara tace mai kuma zai shiga kasuwa cikin ƙanƙanin lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya bayyana cewa man fetur da matatar Ɗangote ta tace zai fara shiga kasuwa daga ranar 15 ga watan Satumba, 2024.

Wannan dai na zuwa ne bayan matatar attajirin ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote ta tabbatar da fara tace man fetur a makon nan da ke bankwana.

Kara karanta wannan

Bayan tashin farashin fetur, Naira ta sake shiga matsala a kasuwar canji a Najeriya

Matatar Dangote
NNPC ya ce man matatar Ɗangote zai shiga kasuwa nan da ranar 15 ga watan Satumba, 2024 Hoto: Dangote Group
Asali: Getty Images

Kamfanin NNPCL ya tabbatar da lokacin da za a fara sayar da man Ɗangote a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Alhamis.

NNPCL ya faɗi yadda farashin fetur zai kasance

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na NNPCL, Olufemi Soneye, ta ce yanayin kasuwa ne zai ƙayyade farashin man feturin Ɗangote.

Kazalika sanarwar ta haƙaito mataimakin shugaban sashin kula da ayyukan mai, Adedapo Segun yana cewa an sauya fasalin ɓangaren, ba ruwan kamfani da farashi.

Kalamansa dai sun kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ke yawo cewa NNPCL ne zai ci gaba da ƙayyade farashin mai duk da ya sanar da miƙa sashin ga ƴan kasuwa.

Segun ya ce:

"An sauya tsarin kasuwancin ma'ana dai yanzu yanayin kasuwa ne zai tsaida farashin fetur maimakon NNPCL ko gwamnati. Bugu da ƙari, farashin canji na taka rawa wajen daidaita farashi."

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Yaushe man Ɗangote zai shiga kasuwa?

Dangane da batun fara jigilar mai daga matatar Ɗangote, Mista Segun ya ce NNPCL na jiran wa'adin matatar ta bayar na ranar 15 ga watan Satumba, 2024.

Segun ya ƙara da cewa babu wani mutum mai cikakken hankali da tunani da zai ji dadin karancin man feturin da ake fama da shi a halin yanzu. 

Ya ce NNPCL na da kusan gidajen mai guda 1000 a fadin kasa kuma tuni ya fara hada gwiwa da ‘yan kasuwa don “tabbatar da buɗe gidajen mai da wuri da tashi a makare."

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen samar da isasshen feturin da zai biya buƙatun ƴan Najeriya.

Gwamnatin Tinubu ta shirya magance ƙarancin mai

A wani rahoton gwamnatin tarayya ta ce nan da karshen makon nan fetur zai wadata saboda haka jama'a su kwantar da hankula.

Karamin ministan fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana hakan bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262