Zargi Ta'addanci: Yan Sanda Sun Sa Sabuwar Ranar Ganawa da Shugaban NLC Karo Na 3

Zargi Ta'addanci: Yan Sanda Sun Sa Sabuwar Ranar Ganawa da Shugaban NLC Karo Na 3

  • Rundunar yan sandan kasar nan ta sanya sabuwar ranar da ta ke bukatar shugaban NLC, Joe Ajaero ya bayyana gabanta
  • Wannan ya biyo bayan fatali da gayyata ta biyu da rundunar ta yi wa Kwamred Ajaero da sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja
  • Rundunar yan sanda kasar nan na tuhumar su da dangantaka da dan Burtaniya, Andrew Wynne a kokarin kifar da gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Rundunar yan sandan kasar nan ta bukaci shugaban kungiyar kwadago na kasa (NLC), Joe Ajaero da ya bayyana gabanta ranar 25 Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Kisan mutum 87: Gwamna ya damu, ya shiga ganawar sirri da babban hafsan tsaro

Wannan ya biyo bayan kin halartar zama da biyu da yan sandan su ka bukata a shelkwatarsu ranar Alhamis, 5 Satumba, 2024.

Kwadago
Yan sanda za su gana da shugaban NLC Hoto: Nigerian Police/Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar ta gayyaci Joe Ajaero da sakataren NLC na kasa, Emmanuel Ugboaja domin tambayoyi kan zargin hadin baki da dan Burtaniya, Andrew Wynne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kin bayyanar Ajaero ga 'yan sanda

Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugabannin kungiyar NLC ba su amsa gayyatar rundunar yan sanda ba domin ci gaba da yi masu tambayoyi kan tuhumar ta'addanci.

Majiya daga rundunar ta bayyana cewa dama shugabannin NLC sun sanar da yan sandan cewa ba za su samu damar halartar zaman ranar Alhamis ba, sai dai a daga.

An fadi dalilin daga zama da 'yan sanda

A ranar Laraba, lauyan NLC, Femi Falana SAN ya ce akwai yiwuwar jagororin kungiyar kwadago su nemi dage zama da yan sanda saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

"Ku kuka yaudari 'yan kasa ba Tinubu ba": An caccaki NLC bayan kara kudin fetur

Falana SAN ya ce shugabannin na da wani aiki da za su yi a wajen babban birnin tarayya Abuja a ranar.

'Yan sanda sun gayyaci Ajaero

A wani labarin, kun ji cewa rundunar yan sandan kasar nan ta sake gayyatar shugaban kungiyar kwadaga (NLC), Joe Ajaero ya sake bayyana a gabanta kan zargin daukar nauyin ta'addanci.

Gwamnatin Najeriya na zargin NLC da Ajaero na da alaka mai karfi da dan asalin Burtaniya, Andrew Wynne a kokarinsu na amfani da zanga-zanga wajen kifar da gwamnatin Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.