Dattawan Yarabawa Sun Yi Adawa da Karin Kudin Fetur, Sun Aika Sako ga Tinubu

Dattawan Yarabawa Sun Yi Adawa da Karin Kudin Fetur, Sun Aika Sako ga Tinubu

  • Majalisar Dattawan Yarabawa ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta kawo karshen wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta
  • Dattawan Yarabawa sun bayyana damuwa kan karin kudin fetur da NNPCL ya yi, tana mai cewa hakan zai kara jefa 'yan kasar a wahala
  • Kungiyar YCE ta jaddada cewa ‘yan Nijeriya na cikin wahala matuka a yanzu, tana mai cewa "babu wuta, babu mai, kuma babu abinci"

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Majalisar Dattawan Yarabawa (YCE) ta bayyana damuwarta kan halin da al’ummar kasar ke ciki, kamar yadda ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta daukar mataki.

Dattawan Yarabawan sun yi magana ne a daidai lokacin da kamfanin NNPCL ya yi karin kudin fetur, lamarin da kungiyar YCE ta ce zai kara jefa mutane a wahala.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Dattawan Yarabawa sun yi magana kan karin kudin fetur
Dattawan Yaraba sun bukaci Tinubu ya gaggauta daukar mataki bayan kara kudin fetur. Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Getty Images

Yarabawa na kuka da tsadar rayuwa

Kungiyar YCE, a cikin wata sanarwa da babban sakatarenta, Oladipo Oyewole ya fitar, ta ce har yanzu tana da yakinin za a samu sauyi mai kyau a kasar nan, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar dattawan Yarabawan ta ce:

“YCE na da yakinin cewa Najeriya za ta samu sauyi. Amma la'akari da matakan da gwamnati ke dauka, a halin yanzu ana tsananin shan wahala a cikin kasar nan.
“Ba tare da samar da wutar lantarki ba, an kuma sanar da karin kudin man fetur, wanda ba abin da hakan zai haifar illa karuwar wahalar da ake fama da ita a Najeriya."

Dattawan Yarabawa sun aika sako ga Tinubu

Dattawan Yarabawa sun ce ya kamata gwamnatin tarayya ta gaggauta bin duk wata hanya da za ta samar wa jama’a sauki da kuma romom dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya tsira": Miyagu sun fasa ofishin gwamnan APC, sun yashe kaya

"Ba ta hanyar rarraba tallafi ba, sai dai ta hanyar samar da hanyoyin inganta rayuwar jama'a da kuma gudanar da ingantaccen shugabanci.
“Ba tare da bata lokaci ba, muna fatan shugaban kasa zai sake waiwayar kundin manufofinsa domin daukar matakan da za su biya bukatun ‘yan Najeriya a wannan lokaci.

Jaridar The Guardian ta rahoto YCE ta jaddada cewa ‘yan Nijeriya na cikin wahala matuka a wannan lokaci, tana mai cewa "babu wuta, babu mai, kuma babu abinci."

Likitoci na so rage kudin fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa likitocin Najeriya karkashin kungiyar NMA sun roki Bola Ahmed Tinubu ya janye karin farashin man fetur da NNPCL ya yi.

Shugaban NMA reshen Legas, Dakta Saheed Kehinde wanda ya ce matsalar tsaro ce ta fara korar likitoci daga kasar nan ya ce karin fetur zai kara ta'azzara lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.