Gwamnan Sokoto Ya Sake Shiri, Ya Tanadi Kayan Aikin Murƙushe Turji da Sauran 'Yan Ta’adda

Gwamnan Sokoto Ya Sake Shiri, Ya Tanadi Kayan Aikin Murƙushe Turji da Sauran 'Yan Ta’adda

  • Gwamnatin Sokoto ta sake shirin fuskantar yan bindiga masu garkuwa da mutane domin kawo karshen ayyukan ta'addanci
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya tanadi karin sababbin motoci da babura da jami'an sa-kai za suyi amfani da su wajen yakar miyagu
  • Gwamnatin ya bayyana yadda ya kamata a yi amfani da motoci da baburan domin samun nasara kan miyagun a yankunan Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Gwamnatin Sokoto ta sake sabon zubin kayan aiki domin fuskantar yan bindiga gadan-gadan.

Gwamna Ahmed Aliyu ya samar da sababbin motoci da babura domin amfani da su wajen kai hare hare a jeji.

Sokoto
An tanadi motoci da babura domin yaki da yan bindiga a Sokoto. Hoto: Hon Naseer Bazzah
Asali: Facebook

Legit ta tabbatar da lamarin ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan Sokoto, Naseer Bazzah ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayan aikin da aka samar a Sokoto

Gwamna Ahmed Aliyu ya tanadi sababbin motoci kirar Hilux guda 20 ga jami'an sa kai na jihar Sokoto.

Haka zalika gwamnatin Sokoto ta samar da babura 710 domin shiga lungu da sako da 'yan bindiga ke aikata ta'addanci.

'Yan sa kai za su yi amfani da motoci da baburan ne a ƙananan hukumomin jihar Sokoto guda 13 da ke fama da tsananin masifar yan bindiga.

An ware kudin gyaran motoci da babura

Kwamishinan kananan hukumomi a Sokoto, Ibrahim Dadi ya ce an tanadi kudi na musamman domin gyaran abubuwan hawan saboda shirin ko-ta-kwana.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za a yi amfani da babura da motocin ne domin yaki da yan bindiga ba hawa domin bukatun yau da kullum ba.

Jagoran 'yan sa-kai na jihar Sokoto, Kanal Musa Na'Allah mai ritaya ya ce za su tabbatar sun yaki yan bindigar yadda ya kamata har su ga bayansu.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

"Dalilin bidiyon Bello Turji" - Gwamnatin Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa bayan ganin sabon bidiyon dan ta'adda, Bello Turji, gwamnatin Sokoto ta yi magana kan dalilin aika-aikar.

An ruwaito cewa gwamnatin Sokoto ta ce Turji ya rikide ne saboda ganin shirin karar da su da Gwamna Ahmed Aliyu ke yi a halin yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng