Hukumar ICPC Ta Titsiye Ministan Buhari, Ana Bincike kan Badakalar Kwangilar NSITF

Hukumar ICPC Ta Titsiye Ministan Buhari, Ana Bincike kan Badakalar Kwangilar NSITF

  • Chris Ngige, tsohon ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya gurfana gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC
  • ICPC ta titsiye Ngige kan zargin ya taka rawa a badakalar kwangiloli da kuma ta daukar ayyuka a lokacin ya ke kan kujerar minista
  • Tsohon ministan ya kasance a gaban jami’an ICPC na tsawon sa’o’i biyar yana amsa tambayoyi kan kwangilolin da aka ba NSITF

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta titsiye Chris Ngige, daya daga cikin ministocin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

An ce ICPC ta yi wa Chris Ngige, wanda ke kula da ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi tambayoyi kan zargin ya taka rawa a badakalar kwangiloli da daukar aiki.

Kara karanta wannan

Gini mai hawa 2 ya rikito a Kano bayan mamakon ruwa, mutane sun kwanta dama

Hukumar ICPC ta titsiye tsohon ministan kwadago da daukar samar da ayyukan yi, Chris Ngige
Tsohon ministan kwadago, Chris Ngige ya gurfana gaban hukumar ICPC. Hoto: @Ihekante
Asali: Twitter

Hukumar ICPC ta titsiye tsohon minista

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana zargin tsohon ministan da sa hannu a karkatar da kudin kwangila a daya daga cikin hukumomin a lokacin da ya rike madafun iko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Chris Ngige ya kasance a gaban jami’an ICPC na tsawon sa’o’i biyar a ranar Laraba domin amsa wasu tambayoyi kan yadda aka bayar da wasu kwangiloli a hukumar inshorar NSITF.

Majiyoyin ICPC da ke da masaniya kan lamarin sun ce an gayyaci Ngige ne domin ya yi bayani kan kwangilar e-NSITF da aka bayar da kuma dalilin watsar da ita.

ICPC na binciken kwangilar NSITF

An rahoto cewa ICPC ta gayyaci wasu manyan jami’an NSITF domin amsa tambayoyi kan biyan N47m na giratuti ga tsohuwar shugaban hukumar, Misis Maureen Allagoa.

Hakazalika, tsohon ministan kwadago, Simon Lalong, ya taba kafa wani kwamiti na musamman domin ya binciki badakalar kwangilar N1.8bn da aka bayar a hukumar.

Kara karanta wannan

ISWAP ta dauki alhakin kashe mutane 87 a Yobe, ta bayyana dalilin kai hari

Tun daga wannan lokacin ne hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ICPC da EFCC suka shiga cikin lamarin inda har ta kai ga an aika gayyaci tsohon ministan.

"Tururuwa ta cinye N17.1bn" - NSITF

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da asusun inshora na Najeriya (NSITF) ta shaida wa majalisar dattawa cewa tururuwa ta cinye takardun N17.158bn.

Wannan na zuwa ne yayin da ofishin babban mai binciken kudi na kasa ya gabatar da korafe-korafe 50 da suka danganci karkatar da N17.158bn da hukumar gudanarwar NSITF ta yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.