Shugaban kasa ya kori Shugaban NSITF bayan ya ci biliyoyin kudi, ya hada shi da EFCC, ICPC

Shugaban kasa ya kori Shugaban NSITF bayan ya ci biliyoyin kudi, ya hada shi da EFCC, ICPC

- Bayo Somefun ya bar kujerar Shugaban Nigeria Social Insurance Trust Fund

- An nada Akabogu Michael bayan an tabbatar cewa Somefun ya saci wasu kudi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsige babban darektan hukumar Nigeria Social Insurance Trust Fund, Bayo Somefun daga matsayinsa.

Jaridar The Nation ta ce tuni har an nada Akabogu Michael a matsayin sabon babban darekta wanda zai gaji Bayo Somefun wanda aka dakatar tun 2020.

Ana zargin tsohon shugaban hukumar da laifin batar da Naira biliyan 3.4 da sunan horas da jami’ai.

KU KARANTA: Buhari ya zabi tsohon SGF ya kawo zaman lafiya a yankin Chadi

A shekarar bara gwamnatin Muhammadu Buhari ta dakatar da Somefun da wasu shugabannin hukumar NSITF uku bisa zarginsu da ake yi da laifin sata.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Sanata Chris Ngige, ya jefi shugabannin NSITF da laifin saba doka wajen bada kwangila da kuma cin kudi.

A wani jawabi da ya fito ta bakin darektan hulda da ‘yan jarida da jama’a na ma’aikatar kwadago, Charles Akpan, shugaban kasa ya tsige majalisar Somefeun.

Tribune ta ce shugaban kasan ya yi aiki da rahoton kwamitin bincike wajen sallamar Somefun, sannan ya bada umarni a sake zubin shugabannin hukumar.

KU KARANTA: Hadimin Shugaban kasa ya fadi dalilin da ya sa ake watsar da kudirorin Majalisa

Shugaban kasa ya kori Shugaban NSITF bayan ya ci biliyoyin kudi, ya hada shi da EFCC, ICPC
Tsohon Shugaban NSITF, Bayo Somefun
Asali: Twitter

Somefun da wasu darektoci uku da aka samu tsamo-tsamo da laifi za su dawo da N181, 056,000 da suka rika zaftara daga cikin albashi da alawus ba da izni ba.

Shugabannin da aka sallama sun yi gaba da wadannan kudi ne da sunan albashi, alawus din zirga-zirga, kudin jirgi, rajistar DSTV da kuma kudin hayar gidaje.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma bada umarni a aika duk wani kamfani ko jami’i da ya ki dawo da kudin da ya sata zuwa gaban hukumomin EFCC da ICPC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng