Ana Kuka da Tsadar Mai, Gwamna a Arewa Ya Cire Tuta Wurin Kawowa Al'ummar Sauki

Ana Kuka da Tsadar Mai, Gwamna a Arewa Ya Cire Tuta Wurin Kawowa Al'ummar Sauki

  • Ana cikin mawuyacin hali bayan kara farashin mai a Najeriya, Gwamnatin jihar Kwara ta agazawa al'ummarta
  • Gwamnatin ta ba da umarnin samar da bas musamman a cikin birni domin zirga-zirgar jama'a wurare daban-daban
  • Gwamnatin jihar ta roki al'umma da masu ababan hawa da su kara hakuri ana neman hanyoyin magance matsalolin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta tallafawa mutane da motocin bas bas saboda tsadar mai.

Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazak ya ba da umarnin samar da bas din domin kwasar mutane kyauta.

Gwamna a Arewa ya kawo sauki ga al'umma bayan kara farashin mai
Gwamnatin Kwara ta samar da bas bas domin tallafawa al'umma bayan kara kudin mai. Hoto: AbdulRahman AbdulRazak.
Asali: Facebook

Kwara: Gwamna ya tallafa kan tsadar mai

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 5 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa zai tura 'ya 'yan talakawa karatu kasar waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi haka ne domin ragewa al'ummar jihar radadin kara farashin mai da aka yi.

Wannan na zuwa ne bayan kara farashin litar mai daga N568 zuwa N897 a gidajen man NNPCL.

Karin farashin man ya sake jefa al'umma cikin halin kunci duk da fama da ake yi a ƙasar.

"An samar da bas bas din domin saukakawa al'umma zirga-zirga musamman a cikin gari."
"Muna fatan wannan mataki zai taimakawa masu zuwa gwajin neman aikin SUBEB da ake yi a jihar."

- Rafiu Ajakaye

Gwamnatin Kwara ta roki al'ummar jihar

Gwamnatin jihar ta roki masu zirga-zirgan ababan hawa da sauran al'umma da su kara hakuri kan karin farashin da aka yi.

Ta ce masu ruwa da tsaki da hukumomin gwamnati suna dukan mai yiwuwa domin kawo sauki ga al'umma.

Gwamnan Kwara zai dauki ma'aikata a jiha

Kara karanta wannan

Sanata a Arewa ya duba halin da ake ciki, ya bayar da tallafin tirela 200 na abinci

Kun ji cewa gwamnatin jihar Kwara ta shirya daukar jimillar ma’aikatan da malaman makaranta 1,600 daga fadin kananan hukumomi 16.

Shugaban hukumar, Farfesa Raheem Adaramaja ne ya bayyana haka ne a ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2024.

A wata sanarwa da sakatariyar yada labaran hukumar, Atere Ameenat ta fitar, ta ce za a ɗauki ma'aikatan ne bisa umarnin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.