"Ba Za Mu Iya Jurewa ba:" Likitoci Sun Roki Tinubu Ya Janye Karin Farashin Fetur

"Ba Za Mu Iya Jurewa ba:" Likitoci Sun Roki Tinubu Ya Janye Karin Farashin Fetur

  • Likitocin kasar nan sun roki shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taimaka a janye karin farashin litar fetur da kamfanin NNPCL ya yi
  • Shugaban kungiyar likitoci ta NMA reshen jihar Legas, Dr. Saheed Kehinde ya bayyana cewa ba za su iya jure karin farashin ba
  • Dr. Kehinde ya kara da cewa tun a baya, matsalar rashin tsaro na sa likitoci ficewa daga kasar nan, kuma karin fetur zai kambama matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Likitoci karkashin kungiyar NMA sun roki Bola Ahmed Tinubu ya janye karin farashin man fetur a kasar nan.

Kara karanta wannan

Shettima ya saka labule da Minista, Ribadu, Kyari yayin da farashin fetur ya kai N1200

Kiran na zuwa kwanaki biyu bayan kamfanin NNPCL ya bayyana karin litar fetur zuwa sama da N800 a sassan kasar nan.

Tinubu
Likitoci sun roki Tinubu ya janye karin farashin fetur Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban NMA reshen jihar Legas, Dr. Saheed Kehinde ya bayyana cewa tun da fari, matsalar tsaro na korar likitoci daga kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin farashin fetur zai jawo matsala

Kungiyar likitoci ta NMA ta bayyana cewa karin farashin litar fetur da aka yi a kasar nan zai kara sa likitoci guduwa zuwa kasashen waje neman aiki.

Channels Television ta wallafa cewa Dr. Kehinde ya ce karin kudin fetur na zuwa a lokacin da yan Najeriya ke cikin mawuyacin hali da tsadar rayuwa da yunwa.

Likitoci sun koka da karin kudin fetur

Kungiyar likitoci ta gargadi Tinubu kan cewa karin kudin fetur zai jawo karuwar damuwa da cututtukan da su ka shafi kwakwalwa har da rasa rayuka.

Kara karanta wannan

"Za mu bi maku hakkin ku," Tinubu ya sha alwashi kan kisan Bayin Allah a Yobe

Kungiyar na ganin karin farashin litar fetur zai kuma kara ta'azzara talauci da tsadar kayan amfanin yau da kullum a Najeriya.

Majalisa ta magantu kan karin kudin fetur

A baya kun ji cewa yan majalisa marasa rinjaye sun bayyana rashin jin dadin yadda kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya bayyana karin farashin litar fetur.

Shugaban yan majalisa marasa rinjaye, Hon. Kingsley Chinda ya bayyana cewa yan kasar nan na rayuwa cikin kuncin tun gabanin kara farashin, saboda su ka nemi a janye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.