Jigo a APC Ya Ba Tinubu Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Yiwa Ministocinsa

Jigo a APC Ya Ba Tinubu Shawarar Abin da Ya Kamata Ya Yiwa Ministocinsa

  • Jigo a jam'iyyar APC, Ibrahim Modibbo ya bayyana cewa ƴan Najeriya na jin raɗaɗin halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi
  • Ibrahim Modibbo ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yana samun gurɓatacciyar shawara kan manufofin gwamnatinsa ga talakawa
  • 'Dan siyasar ya buƙaci shugaban ƙasan da ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul ta hanyar korar kusan da yawa daga cikinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam'iyyar APC, Ibrahim Modibbo, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kori da yawa daga cikin ministocinsa.

Ibrahim Modibbo wanda tsohon daraktan yaɗa labarai ne na Nuhu Ribadu, ya nuna cewa shekara uku ne kacal suka ragewa Tinubu ya sauya akalar gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadawa Tinubu gaskiya kan halin da ake ciki a kasa

An ba Tinubu shawara kan ministoci
Jigo a APC ya bukaci Tinubu ya kori ministocinsa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

"Ya kamata Tinubu ya kori ministoci", Modibbo

Jigon na jam'iyyar APC ya bayyana tawagar masu ba Tinubu shawara kan tattalin arziƙi karƙashin jagorancin Wale Edun a matsayin waɗanda ba su san komai ba a zahiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Modibbo ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da tashar Arise tv wacce Legit Hausa ta bibiya.

"Mutanen da ke tare da shugaban ƙasa suna ba shi gurɓatacciyar shawara. Idan da ni ne shugaban ƙasa a yau sai na kori kusan dukkanin ministocin nan."
"Shugaban ƙasa yana buƙatar ya samu sababbin fuskoki a tattare da shi da sababbin masu ba shi shawara. Saboda ƴan tawagar da ke ba shi shawara kan tattalin arziƙi, a gani na ba su san komai ba."
"Suna tsayawa ne kawai kan abin da suka gani a littattafan tattalin arziƙi ba tare da yin la'akari da tsarin tattalin arziƙin Najeriya, ba su duba talaka wajen yanke hukuncin su."

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya shiga matsala bayan ya yi wa wasu gwamnoni barazana

- Ibrahim Modibbo

Bwala ya buƙaci Tinubu ya kori ministoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa Daniel Bwala, tsohon kakakin yaƙin kwamitin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kori ministocin tsaro.

Bwala ya buƙaci Shugaba Tinubu ya kori Mohammed Abubakar Badaru da Mohammed Bello Matawalle idan aka ci gaba da samun rashin haɗin kai a tsakanin hukumomin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng