Rikicin Wike da Gwamnonin PDP Ya Tsananta, An Sauya Lokacin Taron Kwamitin NWC

Rikicin Wike da Gwamnonin PDP Ya Tsananta, An Sauya Lokacin Taron Kwamitin NWC

  • PDP ta dage taron da ta shirya yi na kwamitin gudanarwarta sakamakon rikicin da ya mamaye jam'iyyar a 'yan kwanakin nan
  • An rahoto cewa shugaban PDP na kasa, Umar Damagum ya dage taron kwamitin gudanarwar zuwa mako mai zuwa saboda rikicin
  • Legit Hausa ta lura an samu karuwar takun saka tsakanin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da kungiyar gwamnonin PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban riko na kasa na PDP, Umar Damagum ya dage babban taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar zuwa mako mai zuwa.

Damagum ya dage taron ne saboda karuwar takun saka tsakanin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da kungiyar gwamnonin PDP, dangane da matsayin zaben jam'iyyar na Ribas.

Kara karanta wannan

Gwamma ya kafa kwamiti, zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000

PDP ta sauya lokacin gudanar da taron kwamitin gudanarwarta
Damagun ya sauya lokacin da PDP za ta gudanar da taron kwamitin gudanarwarta. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Rikicin Wike da gwamnonin PDP

Punch ta tattaro cewa saboda karuwar rikicin da kuma hana tada zaune tsaye a taron kwamitin gudanarwar da aka shirya yi a ranar Laraba, Damagum ya dage taron zuwa mako mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Wike da gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, gwamnonin PDP sun goyi bayan Fubara.

Kungiyar gwamnonin PDP ta bukaci kwamitin gudanarwar PDP da ya amince da Fubara a matsayin jagoran jam’iyyar a Ribas tare da mika masa ragamar tafiyar da ita.

Wannan matsaya da gwamnonin suka dauka ta harzuka Wike, inda ya gargade su da su guji shiga lamarin Ribas ko kuma ya ‘kunno masu wuta’ a jihohinsu.

An dage taron PDP-NWC

An ce Damagum, sakataren PDP na kasa Umar Bature, mataimakin shugaba na kasa, Taofeek Arapaja, mataimakin sakatare, Setoji Kosheodo, sun yi taro a sakatariyar a jam'iyyar, inji rahoton TV360.

Kara karanta wannan

Nenadi Usman: An naɗa mace a matsayin shugabar jam'iyya ta ƙasa a Najeriya

Wata majiya daga jam'iyyar ta ce:

"Babu bukatar taron kwamitin gudanarwa a wannan lokacin. Za a gudanar da taron a mako mai zuwa."

Da aka nemi jin ta bakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagun ya fayyace cewa ba wani taron kwamitin gudanarwa da aka shirya yi.

Wike ya fusata gwamnonin PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin jam’iyyar PDP sun fusata da kalaman Nyesom Wike, ya yi na cewa zai kunno masu wuta a jihohinsu kan rikicin jihar Ribas.

Emmanuel Agbo, darakta-janar na kungiyar gwamnonin PDP, ya nemi hukumomin tsaro da su ankara da furucin ministan Abuja, wanda ya ce kalaman tunzurawa ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.