Kisan Mutum 87: Gwamna Ya Damu, Ya Shiga Ganawar Sirri da Babban Hafsan Tsaro

Kisan Mutum 87: Gwamna Ya Damu, Ya Shiga Ganawar Sirri da Babban Hafsan Tsaro

  • Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya shiga ganawa da babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa bisa kisan mutane
  • A ranar Lahadi ne yan bindiga daga kungiyar ISWAP su ka kai mummunan hari garin Mafa inda su ka kashe mutane akalla 87
  • Buni ya bayyana damuwa kan yadda yan ta'adda su ke shiga jiharsa ta Yobe suna kashe mutane da kone-kone yadda suke so

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - Gwamna Mai Mala Buni ya gana da babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa bisa kisan bayin Allah a Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a Yobe.

Kara karanta wannan

"Kun matsawa masu zanga zanga maimakon 'yan ta'adda," Atiku ya caccaki Tinubu

A ranar Lahadi ne yan kungiyar ISWAP ta ka kai mummunan hari garin, wanda mafi yawansu manoma ne, tare da kashe mutane 87.

Mamman Muhammad
Gwamnan Yobe ya gana ba babban hafsan tsaro kan harin Mafa Hoto: Mamman Muhammed
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, darakta janar kan yada labaran gwamnan, Mamman Mohammed, ya ce Hon. Mai Mala Buni ya bayyana damuwa kan yadda yan ta'adda ke kutsawa yankunan Yobe su na kashe mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yobe: Ana son kawar da ta'addanci

Jaridar Leadership ya wallafa cewa gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa ana neman hanyar magance matsalar ta'addanci a jihar.

Gwamnan ya ce a zantawarsa da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, an tattauna samar da hanyar magance matsalar a Yobe.

Gwamnatin Yobe na aiki da jami'an tsaro

Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ba jami'an tsaro dukkanin taimakon da su ke bukata wajen kakkabe ta'addanci.

Kara karanta wannan

"Za mu bi maku hakkin ku," Tinubu ya sha alwashi kan kisan Bayin Allah a Yobe

A martaninsa, babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa za su kara yawan sojoji a Yobe da zummar dakile hare-haren yan bindiga.

ISWAP ta dauki nauyin harin Yobe

A baya mun ruwaito cewa kungiyar yan ta'addan ISWAP ta dauki alhakin harin da ya kashe jama'a da dama a garin Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Kungiyar ta bayyana cewa ta kai harin ne a matsayin martani da jan kunne ga mazauna Mafa bayan sun zarge su da hada kai da sojoji wajen kashe wasu daga cikin yan ISWAP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.