Zanga Zanga: Kwamitin Gwamnatin Kano Zai Fara Binciken Daidaikun Mutane

Zanga Zanga: Kwamitin Gwamnatin Kano Zai Fara Binciken Daidaikun Mutane

  • Kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa kan rikicin da ya afku lokacin zanga-zanga zai fara gayyatar wadanda ake zargi da tayar da kura
  • Shugaban kwamitin, Alkali Lawan W. Mohmoud Mai ritaya ya ce za a kamo duk wanda ya ki amsa goron gayyatar da aka aika masa
  • Kwamitin zai gudanar da aikinsa ba tare da fargaba ko alfarma ba, domin ta haka za a gano wadanda su ka gurbata zanga-zangar lumanar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi da gurbata zanga-zangar lumana ta kwanaki 10 a jihar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke kan karin kuɗin fetur, an rufe gidajen mai da shaguna

Daga ranar 1 zuwa 10 Agusta, 2024 ne jama'ar kasar nan su ka gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu kan manufofin shugaba Bola Tinubu.

Abba Kabir
Kwamitin binciken zanga zanga zai fara aiki a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa a jawabinsa, shugaban kwamitin binciken zanga zanga, Mai Shari'a Lawan W. Mohmoud Mai ritaya ya ce da gaske su ke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano na binciken rikicin zanga zanga

Punch ta wallafa cewa kwamitin binciken rikicin zanga-zanga a Kano ya ce zai bayar da umarnin cafko duk wanda aka gayyata ya bayyana gabanta kan batun amma ya ki zuwa.

Mai Shari'a Lawan W. Mohmoud Mai ritaya ya bayyana cewa ba za su ji tsoron kowa yayin gudanar da aikin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masu ba.

Ayyukan kwamitin binciken zanga zanga

Mai Shari'a Lawan W. Mohmoud Mai ritaya ya ce wasu daga cikin ayyukan da kwamitinsu zai yi shi ne binciken dalilan rikidewar zanga-zanga zuwa rigima a Kano.

Kara karanta wannan

Gini mai hawa 2 ya rikito a Kano bayan mamakon ruwa, mutane sun kwanta dama

Haka kuma za a gano mutanen da su ka haddasa juyewar zanga-zangar lumana zuwa tashin hankali da irin asarar da aka tafka.

Zanga zanga: Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti

A baya mun ruwaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin da zai yi bincike kan yadda zanga-zanga ta kasance a jihar Kano wacce ta gudana daga 1-10 Agusta, 2024.

Gwamna Abba ya umarci kwamitin da kar ya dagawa kowa kafa yayin binciken irin asarar rayuka da ta dukiyoyi da aka tafka yayin zanga-zangar da kuma wadanda ke da hannu a rikicin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.