Tarewar Hafsoshin Tsaro Arewa Ta Zo da Alheri, Sojoji Sun Yi Rugu Rugu da Miyagu
- Da alamu zuwan Bello Matawalle yankin Arewa maso Yamma ya fara haifar da ɗa mai ido a wajen yaki da ta'addanci
- Da safiyar yau Alhamis 5 ga watan Satumbar 2024 ne sojoji suka hallaka yan bindiga akalla guda biyar a Katsina
- Sojojin sun samu nasarar hallaka miyagun ne a kan hanyar Katsina zuwa Jibia kamar yadda aka yada faifan bidiyon
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Rundunar sojojin Najeriya ta hallaka wasu kasurguman yan bindiga a jihar Katsina.
Sojojin sun yi nasarar kashe miyagun ne da safiyar yau Alhamis 5 ga watan Satumbar 2024.
Katsina: Sojoji sun hallaka yan bindiga
Hadimin Gwamna Dikko Radda a bangaren sadarwa, Isah Miqdad shi ya wallafa bidiyon a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Miqdad ya tabbatar da cewa sojojin sun hallaka yan bindigar ne a kan hanyar Katsina zuwa Jibia da safiyar yau Alhamis.
A cikin faifan bidiyon, an gano mutane suna ta shewa da yabawa jami'an tsaron kan wannan kokari da suka yi.
Har ila yau, a bidiyon an gano yan ta'addan a kwance yayin da daya daga cikinsu ke zaune kafin aka bindige shi.
Yaushe sojoji suka yi ajalin yan ta'adda
"Da safiyar yau Alhamis, sojojin Najeriya sun tunkari yan ta'adda dauke da muggan makamai a kan hanyar Katsina zuwa Jibia inda suka yi nasara hallaka biyar tare da kwace babura da bindigogi kirar AK-47."
- Isah Miqdad
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya isa jihar Sokoto domin yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Yamma.
Matawalle ya tare a Arewa maso Yamma
Kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya umurci babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa da wasu hafsoshin tsaro su koma jihar Sokoto.
Shugabannin sojojin za su kula da hare-haren sojoji kan 'yan ta'addan daga Sokoto, da nufin dakilewa da kawo karshen ta’addanci a Arewa maso Yamma.
Wannan umarnin ya kuma biyo bayan hare-haren 'yan bindiga da suka yi kamari a jihar Sokoto, ciki har da kisan wani basarake a kwanan baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng