"Kun Matsawa Masu Zanga Zanga Maimakon 'Yan Ta'adda," Atiku Ya Caccaki Tinubu

"Kun Matsawa Masu Zanga Zanga Maimakon 'Yan Ta'adda," Atiku Ya Caccaki Tinubu

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta maida hankali kan abubuwa marasa amfani
  • Atiku na magana ne kan karuwar rashin tsaro a kasar nan, amma gwamnati ta fi nuna damuwa kan yan zanga-zangar adawa da yunwa
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar nan ya kuma yi tir da harin da miyagu su ka kai jihar Yobe wanda ya kashe mutane sama da 87

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na mayar da hankali kan abin da ba zai amfani kasa ba.

Kara karanta wannan

Gini mai hawa 2 ya rikito a Kano bayan mamakon ruwa, mutane sun kwanta dama

Ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi kokarin mayar da hankali kan tsaro ba wai takurawa wadanda su ka yi zanga-zangar adawa da yunwa a kasar nan ba.

Atiku
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Tinubu kan tsaro Hoto: Atiku Abubakar/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana cewa duk da kashe-kashen jama'a a Arewa maso Gabas da Arewa ta Yamma, gwamnati ta yi biris da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya yi tir da kisan Yobe

Channels Television ta bayyana cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan bayin Allah a Yobe.

A ranar Lahadi ne miyagu su ka kai hari a wani yanayi na kisan kare dangi kan manoma a jihar Yobe, tare da kashe mutane 87.

"Gwamnati ta gaza a bangaren tsaro" - Atiku

Kara karanta wannan

An gano yadda ake shigo da makamai Najeriya, gwamnati ta dauki mataki

Jagora a jam'iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa kisan da miyagu suka yi a Yobe ya nuna gazawar gwamnati a bangaren tsaro.

Yayin mika ta'aziyyarsa ga mazauna jihar Yobe, musamman iyalan wadanda iftila'in ya rutsa da su, Atiku ya shawarci Tinubu ya nemo mafita kan tsaro.

Zaben 2027: Atiku na neman hadin kai

A baya mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta ce akwai magana mai karfi na kokarin hada kan manyan yan siyasar kasar nan uku domin tunkarar babban zabe na gaba.

PDP ta bayyana cewa akwai tattaunawa da ake yi tsakanin Atiku Abubakar, Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso domin hadewa kafin zaben 2027 inda ake fatan kayar da APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.