“Kowa Ya Shirya Sake Fita Zanga Zanga”: Ministan Buhari Ya Soki Malamai
- Tsohon Ministan wasanni da matasan Najeriya, Solomon Dalung ya caccaki malaman addini kan kokarin hana zanga-zanga
- Dalung ya ce yanzu da aka kara kudin mai da yawansu da kafa za su rika yawo saboda haka da kansu za su shiga zanga-zanga
- 'Dan siyasar ya bukaci 'yan Najeriya ka da su karaya, za a ayyana zanga-zangar gama-gari saboda ba za a yarda da zalunci ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung ya soki malaman Musulunci da Kiristoci da suka hana zanga-zanga a Najeriya.
Tsohon Ministan ya ce yanzu da aka kara kudin mai kowa zai ji a jikinsa kuma Fastoci da malamai kowa zai koma tafiya da kafa.
Zanga-zanga: Dalung ya bukaci sake hawa tituna
Dalung ya bayyana haka ne a jiya Laraba 4 ga watan Satumbar 2024 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Ministan ya ce abin takaici ne yadda malaman Kirista suka hana goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi kuma suka je gidan Tinubu da dare.
Ya ce Fastoci sun kai ziyara wurin Tinubu inda bayan dawowarsu suka fadawa mabiyansu cewa ka da su yi zanga-zanga saboda na Musulmai ne.
Dalung ya ce malamai sun taka rawa
"Fastoci da suka hana a zabi tikitin Musulmi da Musulmi sun tafi da dare zuwa gidan Tinubu inda suka rubuta wasiku a majami'u cewa zanga-zanga ta Musulmi ce a bar su da ita."
"Abin kunya ne kuna kiran kanku shugabanni har ku kawo irin wannan maganganu, yunwa ko talauci yana da addini ko kabila ne."
"To yanzu Tinubu da kuka hadu da shi dole za ku fita zanga-zanga saboda an kara kudin mai zuwa N800 domin da yawanku da kafa za ku rika tafiya."
- Solomon Dalung
Dalung ya ce Fastoci bai kamata su yi haka ba domin ganin Musulmai sun yi tikitin Musulmi da Musulmi tun da yanzu sun gane akwai matsala.
'Dan siyasar yake cewa ya kamata Kiristoci su marawa sauran jama'a baya a yaki zalunci.
An soki Dalung kan goyon bayan zaga-zanga
Kun ji cewa Kungiyar Arewa Progressives for Good Governance ta caccaki tsohon Ministan matasa, Solomon Dalung kan zanga-zanga.
Kungiyar ta ce duk wani dan Arewacin Najeriya da ke kiran zanga-zanga ba shi da adalci saboda bai yi a mulkin Muhammadu Buhari ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng