Kudin Man Fetur: Cacar Baki Ya Kaure Tsakanin 'Yan Kwadago da Gwamnatin Tinubu

Kudin Man Fetur: Cacar Baki Ya Kaure Tsakanin 'Yan Kwadago da Gwamnatin Tinubu

  • Kungiyar kwadago ta dauki zafi bayan gwamnatin tarayya ta musa cewa ta yi alkawari da yan kwadago kan kudin mai
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta yi magana ne bayan NLC ta ce gwamnatin tarayya ta yaudareta kan karin kudin mai da aka yi
  • An wayi gari a ranar Talata ne da samun karin kudin mai a gidajen mai mallakar gwamnatin tarayya a dukkan fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Cacar baki ya kaure tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar kwadago kan maganar ƙarin kudin mai.

Kungiyar kwadago ta yi zazzafan martani ga gwamnatin tarayya bayan gwamnati ta musa yin alkawari kan karin kudin mai.

Kara karanta wannan

Yan kwadago sun dauki zafi kan karin kuɗin mai, sun yi umarnin gaggawa ga Tinubu

Yan kwadago
Yan kwadago sun yi martani ga gwamnati kan kudin mai. Hoto: @NLCHeadquarters, @DOlusegu
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanan da kungiyar kwadago ta yi ne a cikin wani sako data wallafa a shafinta a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rikicin yan kwadago da gwamnati

Tun bayan cire tallafin man fetur a 2023 yan kwadago suke jiran gwamnatin tarayya ta yi karin albashi.

Kungiyar kwadago ta ce ta cimma matsaya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi na N70,000 da cewar ba za a kara kudin man fetur a Najeriya ba.

Bayan karin kudin man fetur da aka samu a ranar Talata, gwamnatin Tinubu ta ce sam ba ta yi alkawarin rashin karin kudi da yan kwadago ba.

Yan kwadago sun yi martani ga gwamnati

Yan kwadago sun fusata bayan musa maganar alkawarin karin kudin mai da gwamnatin tarayya ta yi inda NLC ta ce karya fure ta ke ba ta 'ya'ya.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

NLC ta ce tana tunanin gwamnatin tarayya tana da cutar mantuwa ne kasancewar za ta musa alkawarin da suka yi yayin maganar ƙarin albashi.

Joe Ajaero ya ce maganar ta yi kama da wasan yara amma duk da haka za su cigaba da zama a kan matsayar da suka yanke kan lamarin.

An yi zanga zangar karin kudin mai

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Delta a Kudancin Najeriya sun nuna matasa sun yi zanga zangar karin kudin mai.

An ruwaito cewa matasan sun toshe hanyoyi wanda hakan ya kawo tsaiko kan harkokin kasuwanci a yankin da abin ya faru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng