Gini Mai Hawa 2 Ya Rikito a Kano bayan Mamakon Ruwa, Mutane Sun Kwanta Dama

Gini Mai Hawa 2 Ya Rikito a Kano bayan Mamakon Ruwa, Mutane Sun Kwanta Dama

  • Mamakon ruwan sama da aka yi a jihar Kano ya cika wani gidan bene mai hawa biyu, wanda ya jawo faduwarsa a ranar Alhamis
  • Masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da mutane biyu daga baraguzan ginin, yayin da wasu guda biyu suka riga mu gidan gaskiya
  • Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da afkuwar iftila'in, inda ya ce wasu na asibiti

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mutane biyu sun rasu bayan wani gini mai hawa biyu ya fado masu a Nomansland da ke karamar hukumar Fagge da a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano da Kaduna sun hada kai, an ceto budurwa da ta kwana 35 hannun miyagu

Haka kuma an yi nasarar ceto wasu mutane biyu da rai daga karkashin baraguzan ginin da ya rikito da misalin 2.00n.s.

Kano map
Gini ya danne mutane a Kano, an rasa rayuka Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da afkuwar iftila’in.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Ruwa ya yi sanadin rushewar gini

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa wani gini mai hawa biyu ya ruguje bayan an kwana ana ruwa, kuma ruwan ya rasa hanyar fita daga gidan.

Kwarya-kwaryar bincike ya nuna cewa da mamakon ruwan da aka rika yi a baya, kawai sai aka ji gidan ya fado da misalin 2.00n.s, Vanguard News ta wallafa.

Mamakon ruwa ya jawo asara a Kano

Akalla mutane 31 ne su ka riga mu gidan gaskiya a jihar Kano sakamakon ambaliyar ruwa a damunar bana da har yanzu ake ciki.

Kara karanta wannan

"Rudewa suka yi," Bature ya yi martani kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kano ce ta tabbatar da haka a ranar Laraba, inda ta kara da cewa gidaje sama da 5,280 ne su ka ruguje.

Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a Kano

A baya kun ji cewa hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Kano ta bayyana irin asarar da ambaliyar ruwa ke ci gaba da jawo wa sakamakon mamakon ruwan sama da ake sha.

A kalaman shugaban hukumar SEMA na Kano, Isyaku Kubarachi ambaliyar ta shafi mutane sama da 30,000 a kananan hukumomi 21 daga cikin 44 da ake da su a fadin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.