'Yan Majalisa Sun Yi Martani kan Karin Kudin Fetur, Sun Ba Gwamnati Shawara

'Yan Majalisa Sun Yi Martani kan Karin Kudin Fetur, Sun Ba Gwamnati Shawara

  • Ƴan majalisa marasa rinjaye na majalisar wakilai sun yi Allah wadai da ƙarin kuɗin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi
  • Shugaban marasa rinjayen, Kingsley Chinda, a wata sanarwa ya bayyana cewa ƙarin bai da ce ba duba da halin da ake ciki
  • Sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta sanya baki ta hanyar sauya ƙarin na kuɗin man fetur da kamfanin na NNPCL ya yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar marasa rinjaye ta majalisar wakilai ta yi magana kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a Najeriya.

Ƙungiyar marasa rinjayen ta yi Allah wadai da ƙarin farashin man fetur ɗin wanda kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari sakatariyar karamar hukuma, sun hallaka jami'an tsaro

'Yan majalisa sun caccaki karin kudin fetur
Marasa rinjaye na majalisa sun yi Allah wadai da karin kudin fetur Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Ƴan majalisa sun soki ƙarin kuɗin fetur

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Kingsley Chinda, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisar sun bayyana matakin a matsayin wanda bai dace ba, da rashin tausayi kan ƙalubalen tattalin arziƙin da ƴan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ƙarin farashin zai ƙara ta’azzara raɗaɗi ga talakawan Najeriya, wanda zai haifar da tsadar kuɗin sufuri, farashin abinci, da sauran muhimman kayayyaki.

Wace shawara suka ba gwamnati?

Ƴan majalisar sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta sa baki tare da sauya ƙarin farashin, da kuma lalubo hanyoyi masu ɗorewa waɗanda za su farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan, rahoton The Guardian ya tabbatar da zancen.

Marasa rinjayen na majalisa sun ba da shawarar ba da fifiko wajen gyarawa da inganta matatun mai na cikin gida, da daƙile cin hanci da rashawa a ɓangaren man fetur, da tabbatar da cewa tallafi yana amfanar da talakawa.

Kara karanta wannan

Karin kudin fetur: NLC ta fusata, ta bayyana muguwar yaudarar da Tinubu ya yi mata

MAN ta koka kan tsadar fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar masu masana'antu a Najeriya (MAN) ta bayyana cewa da yiwuwar farashin kayayyaki su ƙara hauhawa sakamakon ƙarin farashin man fetur.

Wannan na zuwa ne bayan an samu tashin farashin litar man fetur daga N568 zuwa kusan N855 a gidajen mai mallakin kamfanin NNPC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng