TUC Ta Yi Fatali da Ƙarin Farashin Man Fetur, Ta Aika Sakon Gaggawa ga Bola Tinubu
- Ƙungiyar kwadago TUC ta yi fatali da ƙarin farashin man fetur a Najeriya, ta ce duk wahalar a kan ma'aikatan kasar za ta ƙare
- Shugaban TUC, Festur Osifo ya bukaci gwamnatin tarayya ta soke ƙarin nan take kana ta maida hankali wajen farfaɗo da Naira
- Kwamared Osifo ya ce ƙungiyar TUC za ta ci gaba da fafutukar kare haƙƙi da muradan ma'aikata domin tabbatar da walwalarsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kungiyar ‘yan kwadago (TUC) ta yi fatali da karin farashin man fetur da aka yi kwanan nan daga N568 zuwa sama da N800 a Najeriya.
TUC ta bayyana cewa wannan ƙarin babbar illa ce domin zai kara jefa ma'aikata cikin ƙangin talauci da wahalar rayuwa.
Channels tv ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo ya fitar ranar Laraba, 4 ga watan Satumba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TUC ta aika saƙo ga Shugaba Tinubu
Shugaban TUC ya yi kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta janye wannan matakin da ta ɗauka na kara farashin mai.
Ya buƙaci ta maida hankali wajen bullo da tsare-tsaren da za su karawa Naira daraja da yaye wahala da kuncin da ƴan Najeriya suke ciki, rahoton Leadership.
Kwamared Festua Osifo ya ce ɗaukar irin waɗannan matakin ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki ba ya kara nuna rashin damuwar gwamnati da walwalar jama'a.
Ƙungiyar kwadago za ta kare walwalar ma'aikata
"Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta soke ƙarin, kana ta ɓullo da manufofin da za su karfafa Naira da daukar kwararan matakai don rage radadin da ‘yan Najeriya ke ciki.
"TUC ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen kare haƙƙi da muradan ma'aikata a Najeriya kuma za ta ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da adalci, albashi da wurin aiki mai kyau ga ma'aikata," in ji Osifo.
NLC ta ce Tinubu ya yaudari ƴan Najeriya
A wani rahoton kuma ƙungiyar ƙwadago (NLC) ta yi martani mai zafi kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar nan a farkon makon nan
NLC ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya yaudare ta tare da sauran ƴan Najeriya sakamakon ƙarin kuɗin fetur da aka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng