Gwamna Ya Amince da Ƙara Wa Ma'aikata Albashi Ana Tsaka da Batun Tashin Farashin Mai

Gwamna Ya Amince da Ƙara Wa Ma'aikata Albashi Ana Tsaka da Batun Tashin Farashin Mai

  • Yayin da ake fama da tashin farashin fetur, gwamnan jihar Ebonyi ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
  • Gwamna Francis Nwifuru ya yi bayanin cewa sabon albashin ba yana nufin kowane ma'aikaci zai samu ƙarin N70,000 a albashinsa ba ne
  • Nwifuru ya ba da tabbacin cewa a shirye yake ya yi biyayya ga hukuncin kotun ƙolin Najeriya na ƴantar da ƙananan hukumomin jihohi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi Francis Nwifuru ya amince da biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a jihar da ke Kudu maso Gabas.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wasu ‘yan jarida a sabon gidan gwamnati da ke Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

TUC ta yi fatali da ƙarin farashin man fetur, ta aika sakon gaggawa ga Bola Tinubu

Gwaman Francis Nwifuru.
Gwamnatin Jihar Ebonyi za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Facebook

Gwamna ya faɗi ma'anar albashin N70,000

Nwifuru ya yi bayanin cewa N70,000 da aka amince a matsayin albashi mafi ƙankanta ba ƙarin albashi aka yiwa ma'aikata ba, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar gwamnan, dokar na nufin ƙaramin ma'aikaci zai karbi akalla N70,000 duk wata, ba wai ana nufin kowane ma'aikaci zai samu ƙarin N70,000 ba ne.

Ya kuma umurci shugaban ma’aikatan jihar da ya tsara hanyoyin za a bi wajen fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashin.

Yadda ma'aikatan Ebonyi za su fara karɓan N70,000

A ruwayar Tribune, Gwamna Nwifuru ya ce:

"Akwai bambanci tsakanin mafi ƙarancin albashi da ƙarin albashi. Shi mafi karancin albashi ba shi ne karin albashi ba, ba wai N70,000 za a kara wa albashin kowane ma'aikaci ba.
"Ba haka ake nufi ba, shi mafi ƙarancin albashi na nufin albashin da ƙaramin ma'aikaci zai ɗauka, amma kowane ma'aikaci zai amfana."

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga tsaka mai wuya, jam'iyya ta fara shirin ɗaukar mataki a kansa

"Gwamnatin Ebonyi za ta biya N70,000, da zaran shugaban ma'aikata ya tsara yadda za a bi kuma ya gabatar mun, za mu fara biya."

Nwifuru ya kuma jaddada kudirinsa na yin biyayya ga hukuncin da kotun koli ta yanke na ba kananan hukumomi cikakken ikon cin gashin kansu.

Gwamna Kefas ya fara shirin biyan N70,000

A wani rahoton kuma Gwamna Agbu Kefas ya ce tuni gwamnatinsa ta fara shirin biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Kefas ya sanar da hakan ne a gidan gwamnatinsa da ke Jalingo jim kaɗan bayan rattaɓa hannu kan dokar ƙarin kasafin kuɗin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262