An Bukaci Tinubu Ya Kori Manyam Ministoci 2 a Gwamnatinsa, an Fadi Sunayensu

An Bukaci Tinubu Ya Kori Manyam Ministoci 2 a Gwamnatinsa, an Fadi Sunayensu

  • Tsohon hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Barista Daniel Bwala, ya yi tsokaci game da harkar tsaro a yau
  • Bwala ya ba da shawara ya kamata Bola Tinubu ya kori Mohammed Badaru da Bello Matawalle idan abubuwa suka ci gaba da taɓarɓarewa
  • A cewar Bwala, kuskuren Badaru da Matawalle ya sanya ƴan bindiga suka ƙwace motoci masu sulke na sojojin Najeriya a jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Daniel Bwala, tsohon kakakin yaƙin kwamitin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kori ministocin tsaro.

Bwala ya buƙaci Shugaba Tinubu ya kori Mohammed Abubakar Badaru da Mohammed Bello Matawalle idan aka ci gaba da samun rashin haɗin kai a tsakanin hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Farashin Fetur: Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga kungiyar ƙwadago NLC

An bukaci Tinubu ya kori Matawalle
Bwala ya bukaci Tinubu ya kori ministocin tsaro Hoto: Dr Bello Matawalle, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake so Tinubu ya kori ministocin?

Bwala ya yi wannan kiran ne bisa abin da ya bayyana a matsayin rashin haɗin kai tsakanin sojoji da sojojin sama.

Kalaman na Daniel Bwala dai na zuwa ne bayan wasu ƴan bindiga sun yi iƙirarin ƙwace motoci masu sulke na sojojin Najeriya.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fito ta musanta cewa ƴan bindigan ƙwace motocin suka yi.

"Idan har aka ci gaba da samun irin wannan rashin haɗin kan a tsakanin sojoji da sojojin sama, inda muka ga kura-kuran da suka jawo tsagerun ƴan bindiga suka ƙwace motocin mu masu sulke da alburusai. Lallai akwai buƙatar a kori ministocin tsaro."

- Daniel Bwala

Kara karanta wannan

Wike ya aika sako mai zafi ga masu adawa da kasancewarsa a gwamnatin Tinubu

Tinubu ya yi alhini kan harin Yobe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ta bayyana takaicin harin yan kungiyar ISWAP da ya salwantar da rayukan mazauna Mafa, a karamar Tarmuwa a jihar Yobe.

Shugaban kasar ya kuma mika ta'azziyya ga iyalan wadanda aka kashe da sauran mutanen Yobe kan mummunan harin.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da an hukunta miyagun 'yan kungiyar ISWAP da suka kashe mutane 87 a Yobe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng