Matasa Sun Barke da Zanga Zanga kan Ƙarin Kudin Man Fetur, Sun Toshe Hanyoyi

Matasa Sun Barke da Zanga Zanga kan Ƙarin Kudin Man Fetur, Sun Toshe Hanyoyi

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Delta a Kudancin Najeriya sun nuna cewa wasu matasa sun yi zanga zangar karin kudin mai
  • An ruwaito cewa matasan sun toshe hanyoyi wanda hakan ya kawo tsaiko kan harkokin kasuwanci a yankin da abin ya faru
  • Matasan sun fara zanga zangar ne bayan kamfanin NNPCL ya kara kudin fetur a gidajen man gwamnatin Najeriya a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Matasa a jihar Delta sun yi zanga zangar adawa da karin kudin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi a ranar Talata.

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun toshe hanyoyin da al'umma suke wucewa domin zirga zirga.

Kara karanta wannan

Yadda ake zargin yunwa na kashe fursunoni a gidajen yarin Najeriya

zanga zanga
An yi zanga zangar tsadar mai a Delta. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa cikin masu zanga zangar akwai masu aikin Keke NAPEP da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zanga zangar karin kudin mai

A safiyar yau Laraba ne matasa suka fito zanga zangar adawa da tsadar man fetur a jihar Delta da ke Kudancin Najeriya.

DW Hausa ta wallafa cewa matasan sun koka kan tsadar man fetur ne kuma sun yi zanga-zangar ne a karamar hukumar Warri ta Kudu.

Yadda aka yi zanga zangar kudin mai

An fara zanga zangar ne da sassafe inda daruruwan masu Keke NAPEP suka toshe hanyoyin wucewa.

Masu Keke NAPEP sun rika rera wakokin da ke nuna kudin mai ya yi yawa kuma ba za su iya cigaba a haka ba.

Shugaban masu zanga zangar, Samuel Okoro ya ce suna ƙoƙarin rufawa kansu asiri sai ga shi an kara kudin mai da zai kara jefa su a matsala.

Kara karanta wannan

Yan kwadago sun dauki zafi kan karin kuɗin mai, sun yi umarnin gaggawa ga Tinubu

Masu shaguna sun koka da zanga zanga

Masu zanga zangar sun toshe hanyoyi wanda hakan ya jawo tsaiko a harkokin kasuwanci a Warri ta Kudu.

Wani dan kasuwa, Evans Koko ta ce yau ba su samu kasuwa sosai ba saboda mutane ba su samu damar wucewa zuwa shaguna ba.

Kudin mai: An yi zanga zanga a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa zanga zangar adawa da karin kudin mai ta barke a jihar Kano bayan kamfanin NNPC ya yi karin kudi.

An rahoto cewa daruruwan masu sana’ar adaidaita sahu suka mamaye titunan Kano domin nuna fushinsu kan karin kudin da aka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng