Mataimakin Shugaban Kasa Ya Shiga Taron NEC da Manyan Attajirai 2, Bayanai Sun Fito

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Shiga Taron NEC da Manyan Attajirai 2, Bayanai Sun Fito

  • Sanata Kashim Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arziki NEC a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Bayanai sun nuna Ɗangote da attajitin nan, Bill Gates sun halarci taron wanda ya gudana ranar Laraba, 4 ga watan Satumba
  • Gwamnan Borno, Babagana Umaru Zulum da takwaransa na Bauchi, Bala Mohammed na cikin waɗanda suka je taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima na jagorantar taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) yanzu haka a Aso Rock da ke birnin Abuja.

Bayanai sun nuna cewa an gayyaci shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote domin ya halarci taron na yau Laraba.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Kashim Shettima ns jagorantar taron NEC a Aso Villa Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Kazalika an gayyaci hamshaƙin attajirin nan kuma shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Bill Gates wanda ya zo ziyara Najeriya, domin halarci zaman NEC, The Nation ta kawo.

Kara karanta wannan

Jihohi 4 sun shiga matsala, Tinubu ya ba su wa'adin kwanaki 5 kan kafa 'yan sandan jiha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa NEC ta kira wannan zama?

Majalisar ƙoli ta tattalin arziki NEC na gudanar taron a ranar da ba a saba ba (Laraba) saɓanin ranakun da majalisar ke zama watau Alhamis.

Sai dai har kawo yanzu ba a bayyana maƙasudin kiran wannan taro a wannan rana ba.

Majalisar NEC dai ta kunshi gwamnoni 36 na jihohin Najeriya, gwamnan babban banki CBN da kuma wasu manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya.

NLC ta fusata da ƙarin farashin fetur

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ke zargin gwamnatin tarayya da karya alkawarin da ta yi na kin kara farashin man fetur.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce kungiyar ta amince da mafi karancin albashi na ₦70,000 a watan Yuli bisa tabbacin da gwamnati ta bada cewa ba za a kara farashin mai ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga tsaka mai wuya, jam'iyya ta fara shirin ɗaukar mataki a kansa

Dalilin gayyatar Bill Gates taron NEC

Bugu da ƙari an tattaro cewa Bill Gates ya ziyarci Najeriya ne a wani bangare na yunƙurin gidauniyarsa na bada gudummuwa wajen haɓaka Afirka, rahoton Daily Trust.

Wata majiya ta ce Bill Gates ya halarci taron domin yin jawabi ga NEC kan batutuwan da suka shafi abinci mai gina jiki da kuma rigakafi.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka halarci taron sun hada da na Bauchi, Bayelsa, Borno, Ebonyi, Nasarawa, da Zamfara.

Rahotanni sun ce wasu gwamnonin ba su iya zuwa ba, mataimakansu suka wakilce su.

Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin NLC

A wani rahoton kuma fadar shugaban ƙasa ta musanta ikirarin ƴan kwadago cewa Bola Tinubu ya karya alƙawarin da ya ɗauka kan farashin mai.

Kungiyar kwadago, NLC ta bayyana cewa Tinubu ya yi masu alkawarin ba za a ƙara farashin fetur ba kafin amincewa da albashin N70,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262