Yan Kwadago Sun Dauki Zafi kan Karin Kuɗin Mai, Sun yi Umarnin Gaggawa ga Tinubu

Yan Kwadago Sun Dauki Zafi kan Karin Kuɗin Mai, Sun yi Umarnin Gaggawa ga Tinubu

  • Kungiyar kwadago ta yi magana bayan karin kudin mai da aka yi a gidajen mai mallakin gwamnatin tarayya a fadin Najeriya
  • Shugaban yan kwadago, Joe Ajaero ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta gaggauta rage kudin mai kamar yadda yake a baya
  • Kungiyar NLC ta sanar da shirin yin zama na musamman domin daukan mataki a kan karin kudin mai da kamfanin NNPCL ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar kwadago ta nuna fushi kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kara kudin man fetur.

Shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta janye karin kudin man fetur da ta yi.

Kara karanta wannan

Kudin man fetur: Cacar baki ya kaure tsakanin yan kwadago da gwamnatin Tinubu

Yan kwadago
NLC ta bukaci a rage kudin mai. Hoto: @NLCHeadquarters, @DOlusegun
Asali: Twitter

Legit tattaro bayanan ne a cikin wani sako da kungiyar kwadago ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin kudin mai a Najeriya

A ranar Talata ne aka wayi gari da karin kudin mai a gidajen man gwamnatin tarayya a dukkan jihohin Najeriya.

Ana sayar da litar man fetur ne a Najeriya a kan N617 kafin gwamnatin tarayya ta kara kudin zuwa N897 a ranar Talata.

Hakan ya jawo cece-ku-ce tsakanin yan kasa da kungiyoyin daban daban lura da halin da ake ciki na wahalar rayuwa a Najeriya.

Yan kwadago sun bukaci rage kudin mai

Kungiyar kwadago ta NLC ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta rage kudin mai a Najeriya.

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban yan kwadago, Joe Ajaero ya ce bayan umarnin gaggawan za su yi zama na musamman kan lamarin.

Kara karanta wannan

An kara zuga Tinubu ya lafta haraji a Najeriya, Bill Gates ya ce kudin ya yi kadan

Joe Ajaero ya ce a mako mai zuwa yan kwadago za su zauna kan karin kudin mai kuma za su fadi matakin da suka yanke ga al'ummar Najeriya.

Karin kudin mai: Malami ya yi martani

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna ya nuna fushi kan yadda aka wayi gari da karin kudin man fetur.

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce karin kudin mai a wannan halin da ake ciki ya nuna akwai rashin tausayi a zuciyar shugabannin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng