Sarakunan Kudancin Najeriya Sun Yi Magana kan Kisan Sarkin Gobir, Sun Ba Gwamnati Shawara
- Majalisar sarakunan gargajiya ta Kudancin Najeriya ta yi tofin Allah tsine kan kisan da ƴan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir
- Sarakunan sun yi Allah wadai da kisan gillar da ƴan bindigan suka yiwa marigayi Alhaji Isah Mohammed Bawa kwanakin baya
- Manyan kasar sun kuma koka kan yawaitar kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake samu, suka nemi a shawo kan matsalar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Abia - Majalisar sarakunan gargajiya ta Kudancin Najeriya ta yi Allah-wadai kan kisan da ƴan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isah Mohammed Bawa.
Majalisar ta kuma yi Allah wadai da yawaitar kashe-kashe da sace-sace da ake fama da su a ƙasar nan, inda ta buƙaci gwamnati ta tashi tsaye.
Sarakunan Kudu sun kaɗu kan kisan Sarkin Gobir
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta, mai martaba, Dr Eberechukwu Oji, Eze Aro na masarautar Arochukwu, a Umuahia, babban birnin jihar Abia ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta bayyana kaɗuwarta kan kisan gillar da ƴan bindigan suka yiwa Sarkin na Gobir, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
An yi ta'aziyyar Sarkin Gobir
Yayin da suke nuna alhininsu kan kisan, sun miƙa ta’aziyya ga gwamnatin jihar Sokoto, Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Alhaji Sa’ad Abubakar da iyalan marigayin bisa rasuwarsa.
"Wannan majalisar ta damu cewa waɗannan miyagun makasan ba su fahimci cewa sarakunan gargajiya su ne masu riƙe da al'adu da asalinmu ba, sune gadar da ta haɗa bayanmu da tarihinmu wanda bai kamata a tozarta su ba."
"Haka kuma sarakunan gargajiya ba su ba ne masu kula da dukiyar ƙasa ko suna karɓar kuɗi daga gwamnati wanda hakan zai sanya masu garkuwa da mutane su riƙa fakon su."
- Dr Eberechukwu Oji
Miyetti Allah ta magantu kan kisan Sarkin Gobir
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Miyetti Allah a Najeriya ta yi magana kan kisan Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isa Bawa da yan bindiga suka yi.
Ƙungiyar ta yi Allah wadai da cin zarafi da kuma kisan gillar da ƴan bindigan suka yiwa basaraken a jihar Sokoto inda ta ce abin takaici ne matuƙa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng