Kudin Man Fetur: Malamin Addini Ya Fusata, Ya yi Magana kan Shirya Zanga Zanga
- Wani malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna ya nuna fushi kan yadda aka wayi gari da karin kudin man fetur a fadin Najeriya
- Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce karin kudin mai a wannan halin da ake ciki ya nuna akwai rashin tausayi a zuciyar shugabanni
- Malamin addinin ya kara da cewa ba zai tsawatarwa matasa masu shirin fita zanga zanga saboda tsadar rayuwa a Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Malamin addinin Musulunci a Najeriya ya yi raddi ga gwamnatin tarayya kan karin kudin mai a Najeriya.
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce lamarin ya zo da mamaki lura da halin kuncin rayuwa da ake ciki a Najeriya.
Legit ta tatttaro abin da malamin ya fada ne a cikin wani bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsadar mai da fita zanga zanga
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce ba zai tsawatarwa matasa da suke shirin sake zanga zangar tsadar rayuwa a Najeriya a watan Oktoba ba.
Malamin ya ce shi ba zai yi umarnin fitowa zanga zanga ba, amma duk da haka ba zai soki matasan da za su fito ba.
Karin kudin mai ya sabawa hankali
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce karin kudin mai da aka yi ya nuna cewa kamar gwamantin ba ta cikin hankalinta.
Malamin ya kara da cewa duk wanda ya ba gwamnati shawarar karin kudin mai ba ya son cigaban Najeriya da gwamnatin tarayya.
Buhari bai fi Tinubu ba inji malamin addini
Malam Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce duk da halin da ake ciki babu maganar cewa mulkin Muhammadu Buhari ya fi dama dama a kan mulkin Bola Tinubu.
Sheikh Ibrahim Aliyu ya ce duk halin da ake ciki yana daga cikin abubuwan da gwamnatin Buhari ta shirya a shekarun baya.
NLC ta yi martani kan karin kudin mai
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ƙwadago ta ƙasa ta yi martani mai zafi kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar nan a farkon makon nan.
NLC ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya yaudare ta tare da sauran ƴan Najeriya sakamakon ƙarin kuɗin fetur da aka yi bayan sun gama zama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng