Malamin Addini Ya Fadi Hanyar da Za A Taimakawa Gwamnatin Tinubu

Malamin Addini Ya Fadi Hanyar da Za A Taimakawa Gwamnatin Tinubu

  • Yayin da aka wayi gari a ranar Talata da karin farashin fetur, malamin coci ya shawarci yan Najeriya kan Bola Tinubu
  • Malamin cocin, Rabaran Dr. Michael Akinwale ya ce bai kamata yan Najeriya su rika Allah wadai da gwamnatin APC ba
  • Malamin ya ce abin da ya dace yanzu shi ne yan kasa su dukufa wajen yi wa Tinubu da gwamnatinsa addu'ar nasara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Malamin addinin kirista, kuma jagora a cocin Methodist da ke Abuja, Rabaran Dr. Michael Akinwale ya ce bai dace yan kasar nan su rika kushe gwamnatin Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

"A yi amfani da tsarin IBB": Janar Akilu ya ba Tinubu shawarar magance rashin tsaro

Rabaran Akinwale ya bayyana haka a lokacin da yan Najeriya ke cike da takaicin yadda gwamnatin tarayya ta zura idanu ake samun karuwar farashin man fetur.

Tinubu
Malaman kiristoci sun nemi a yiwa Tinubu addu'a Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa malamin ya ce abin da ya dace yan kasar nan su yi shi ne addu'a, domin neman taimakon Ubangiji a lamarin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan kasa su koma ga Ubangiji" - Rabaran

Malamin addinin kiristan ya ce dole ne shugabanni da talakawan kasar nan su mayar da al'amuransu ga Ubangiji.

Rabaran Michael Akinwale ya bayyana cewa ko a jikin takardar kudin Amurka, an rubuta "da Allah mu ka dogara", Daily Post ta wallafa labarin.

"Ubangiji ne kawai maganin matsalar Najeriya" - Rabaran

Malamin cocin na Methodist a Abuja, Rabaran Dr Akinwale na ganin matsalolin Najeriya sun girmi jagororin kasar sai dai ubangiji.

Rabaran Michael Akinwale ya kara da cewa yin tir da gwamnatin tarayya ba shi ne zai kawar da matsalolin da kasar ke ciki a yanzu ba.

Kara karanta wannan

"Rudewa suka yi," Bature ya yi martani kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu

Malaman kirista sun shawarci Tinubu

A baya kun ji cewa malaman addinin kirista na cocin katolika sun shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta magance matsalolin kasar nan.

Kungiyar malaman ta ce akwai hanyoyi da shugaban ya dace ya bi, kamar bayar da bashi ga manoma da iri mai inganci domin kawo karshen yunwa da tsadar abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.