Ana Jimamin Kashe Mutane 87 a Yobe, 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Jihar Arewa

Ana Jimamin Kashe Mutane 87 a Yobe, 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Jihar Arewa

  • Wasu gungun 'yan bindiga sun kai sabon hari a garin Congo da ke karamar hukumar Bakkos ta jihar Filato inda suka kashe mutane
  • An rahoto cewa 'yan bindigar sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 7 na yammacin Talata a lokacin da mutane ke cin kasuwar garin
  • Wannan harin dai ya kara jawo zaman dari dari a yankin wanda ya ke yawan fuskantar hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane shida a Congo, wani kauye da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki 'yan kwanaki kadan bayan da 'yan ta'adda suka kashe mutane 87 a wani kauyen jihar Yobe.

Kara karanta wannan

ISWAP ta dauki alhakin kashe mutane 87 a Yobe, ta bayyana dalilin kai hari

'Yan bindiga sun farmaki kauyen Congo da ke jihar Filato
'Yan bindiga sun kai sabon hari Filato, sun kashe mutum 6. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki Filato

Wasu majiyoyi daga garin Congo da suka tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, sun ce mutum daya ya samu rauni a harin kuma ya na cikin mawuyacin hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mazauna yankin, lamarin ya faru ne a kasuwar garin da misalin karfe 7 na yammacin ranar Talata, inda ‘yan bindigar suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Yawancin 'yan kasuwa da abokan cinikinsu sun ranta a na kare domin tsira da rayuwasu yayin da rahotanni suka ce an bar wasu 'yan kalilan a baya.

Hare-haren 'yan bindiga sun tsananta a Bokkos

Legit Hausa ta ruwaito cewa lamarin ya sake haifar da tashin hankali a yankin, saboda a ‘yan kwanakin nan ana kai hare-hare a wasu garuruwan karamar hukumar ta Bokkos.

Saboda karuwar rashin tsaro a Bakkos ne mahukuntan jami'ar jihar Filato da ke karamar hukumar suka rufe jami'ar tare da dakatar da jarabawar karshen zango da dalibai ke zanawa.

Kara karanta wannan

Rana ta baci: Mai maganin gargajiya ya kashe mutum wajen gwajin maganin bindiga

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred kan lamarin ba.

'Yan ta'adda sun kai hari a jihar Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu miyagun 'yan ta'adda sun kai hari a kauyen Budel da ke yankin Tangur a karamar Bukkos ta jihar Filato.

An rahoto cewa shugaban karamar hukumar Bukkos, Monday Kassah, ya ce maharan sun shiga garin da daddare, suka ƙona tare da lalata gidaje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.