Za A Yi Ta Ta Kare: Gwamnati Ta Fadi Abin da Ke Shirin Faruwa da Miyagun 'Yan Bindiga

Za A Yi Ta Ta Kare: Gwamnati Ta Fadi Abin da Ke Shirin Faruwa da Miyagun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin tarayya ta ce an shirya tsaf domin koro yan ta'addan da su ka addabi wasu jihohin da ke Arewacin kasar nan
  • An dauki matakin ne domin cika umarnin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ganin an dawo da zaman lafiya a Arewa
  • Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce jami'an tsaro sun shirya, daidai lokacin da jagororin tsaron su ka tare a Sakkwato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a samu saukin ayyukan ta'addanci da ya addabi jihohin Arewacin Najeriya.

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya bayyana cewa an shirya koro miyagun daga maboyarsu a duk inda su ke a Arewa.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa ‘yan Arewa suka mamaye tawagar tsaron Tinubu, Matawalle ya magantu

Matawalle
Gwamnati na shirin kawo karshen miyagu Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bello Matawalle ya ce jami'an tsaro za su cika umarnin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin tsaron sun samu umarnin dawo da zaman lafiya a jihohin Kaduna, Zamfara, Sakkwato da sauran jihohin Arewacin kasar nan.

Sojoji za su kawo karshen miyagun 'yan bindiga

Manyan jami'an sojojin kasar nan, karkashin jagorancin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da babban hafsan sojojin, Janar Christopher Musa sun isa Sakkwato.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugabannin tsaron za su jagoranci sauran sojoji wajen fatattakar miyagun da su ka addabi mazauna Arewacin kasar nan.

Gwamnati za ta taimaka wajen korar 'yan bindiga

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na bayar da dukkanin taimakon da ya dace wajen ganin jami'an tsaro sun kawar da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan ta'ada za su shiga uku, Ministan tsaro da hafsoshin sojoji sun isa Sakkwato

Karamin Ministan tsaro ne ya bayyana haka yayin tunatar da sojoji nauyin da ya rataya a wuyansu a jihar Sakkwato.

Sojoji sun isa Sakkwato don maganin 'yan bindiga

A wani labarin kun ji cewa Bello Matawalle ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa jihar Sakkwato domin cika umarnin shugaba Bola Tinubu.

Shugaban kasar ya bayar da umarnin ga hafsoshin tsaro su koma jihar Sakkwato a yaki yan ta'addan da gaske, har A kawo karshen rashin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.