Gwamnan Sokoto Ya Kashe Naira Biliyan 1.2 wajen Gyara Rijiyoyin Burtsate 25?
- Gwamnatin jihar Sokoto ta fito ta yi karin haske kan batun ba da kwangilar gyaran rijiyoyin burtsatse 25 a kan kudi Naira biliyan 1.2
- A cikin wani faifan bidiyo da ya karade soshiyal midiya, Gwamna Ahmad Aliyu ya ce an kashe makudan kudaden a gyaran rijiyoyin kadai
- Wannan batu dai ya jawo ce-ce-ku-ce sosai, sai dai kwamishinan muhallin jihar ya nuna cewa gwamnan ya yi kuskure ne a kalamansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto na ci gaba da shan suka tun bayan da aka ji shi a bidiyo yana cewa sun kashe Naira biliyan 1.2 a gyaran rijiyoyin burtsatse 25.
Ma'abota soshiyal midiya sun gaza gaskata kalaman gwamnan, inda da wasu ke zargin ko dai gwamnan ya yi kuskure a lissafin ko kuma an karkatar da kudin ne.
Gyara rijiyoyin burtsatsen Sokoto kan N1.2bn
A cikin faifan bidiyon da jaridar The Guardian ta wallafa a shafinta na X, an ji Gwamna Ahmad yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An ba da gyaran rijiyoyin burtsatse har guda 25 a kan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 200."
Wannan na nufin cewa gwamnatin Sokoto ta ba da kwangilar gyara kowace rijiyar burtsatse a kan Naira miliyan 48.
Bayan fitar wannan bidiyo, tsohon mai tallafawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Bashir Ahmed ya yi martani ga kalaman gwamnan:
A shafinsa na X, Bashir Ahmed ya ce:
"Amma Naira biliyan 1.2 na iya samar da rijiyoyin burtsatse guda 1,000."
Kwamishinan Sokoto ya wanke gwamna
Ana tsaka da surutu kan wannan lamari ne sai aka ga bidiyon kwamishinan muhalli na jihar Sokoto, Nura Shehu Tangaza, wanda ya yi karin haske kan kalaman gwamnan.
Nura Tangaza a bidiyon da mai tallafawa Gwamna Aliyu kan kafofin watsa labarai, Hon. Naseer Bazza ya wallafa a shafinsa na X ya ce:
"Wannan aikin an yi shi ne karkashin ma'aikatarsa, kuma ba wai gyara ne za ayi ba, sababbin rijiyoyin burtsatse 25 ne aka ba da kwangilar ginawa."
Kwamishinan ya lissafa wasu garuruwa 5 da aka ba da kwangilar gina rijiyoyin burtsatsen masu amfani da hasken rana a jihar, inda ya ce aikin hadin guiwa ne.
"Aikin hadin guiwa ne tsakanin gwamnatin Sokot da Bankin Duniya. Kuma idan za ku duba duka jihohin da suka ci gajiyar irin hadakar nan, za ku taras duk kudin kusan daya ne.'
- A cewar kwamishinan.
Kalli bidiyon jawabin gwamnan a kasa:
"Ban gaji komai ba" - Gwamnan Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu ya ce bai gaji ko sisin kwabo a baitul malin jihar ba, kuma Aminu Tambuwal bai mika masa ko takardar Naira daya ba.
Gwamnan fadi hakan ne a ganawawarsa da mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya, Benjamin Kanu wanda ya tambaye shi inda ya ke samun kudin ayyukan da ya ke yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng