Gwamnati Ta Fadi Lokacin Ƙarin Kudin Alawus ga Matasa Masu Hidimar NYSC

Gwamnati Ta Fadi Lokacin Ƙarin Kudin Alawus ga Matasa Masu Hidimar NYSC

  • Gwamnatin tarayya ta yi albishir ga masu yi wa ƙasa hidima kan karin kudi yayin da ake maganar sabon mafi ƙarancin albashi
  • Shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ne ya bayyana haka a sansanin masu yi wa ƙasa hidima da ke Kebbi
  • Legit ta tattauna da wata mai hidimar kasa a Jigawa, Ajikanbi Honour Odion domin jin yadda karin kudin zai amfanesu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Hukumar NYSC ta yi albishir ga matasa masu yiwa ƙasa hidima kan maganar ƙarin alawus.

Shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya ce matasan suna kawo cigaba a kasa saboda haka sun cancanta a kara musu alawus.

Kara karanta wannan

"Za mu bi maku hakkin ku," Tinubu ya sha alwashi kan kisan Bayin Allah a Yobe

Masu NYSC
Za a kara alawus din masu NYSC. Hoto: @Officialnyscng
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanan da Birgediya Janar YD Ahmed ya yi ne a cikin wani sako da hukumar NYSC ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a kara kudin 'yan NYSC?

Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana cewa da zarar an fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi za a kara alawus din yan NYSC.

Sai dai shugaban bai ambaci nawa za a dawo biyan matasan ba duk da cewa a yanzu haka ana biyansu N33,000 ne.

YD Ahmed ya yabi 'yan NYSC

Birgediya Janar YD Ahmed ya ce matasa masu yiwa ƙasa hidima sun cancanci yabo yadda suke ba da gudunmawa wajen cigaban Najeriya.

Ya kuma tabbatar masu da cewa hukumar NYSC ba za ta yi sakaci wajen tura su wuraren da babu tsaro ba.

Muhimmacin koyon sana'a ga masu NYSC

Kara karanta wannan

"Na gano mafita," Sarki Sanusi II ya shirya kawo karshen rikicin Fulani a Najeriya

Shugaban hukumar NYSC na kasa ya yi kira ga matasa kan muhimmacin koyon sana'o'in da hukumar ke ba su horo a kai.

Birgediya Janar YD Ahmed ya ce suna haɗaka da bankuna wajen ba matasan da suka koyi sana'o'i bashi domin samun madafa.

Legit ta tattauna da mai hidimar NYSC

Wata mai hidimar kasa a jihar Jigawa, Ajikanbi Honour Odion ta zantawa Legit cewa lallai suna bukatar karin kudin cikin gaggawa.

Ajikanbi ta ce a lokaci daya ta kashe N9,000 a shinkafa tiya biyu wanda hakan ma banda sauran abubuwan da za ta bukata na yau da kullum.

An kubutar da masu NYSC a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta sanar da cewa an samu damar kubutar da 'yan bautar kasar da aka sace a Zamfara.

A shekarar 2023 ne Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan bautar kasar su 8 a kan hanyar Funtua zuwa Gusau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng