An Gaji: Lokuta 3 da Jama'ar Gari Suka Aukawa Miyagun 'Yan Bindiga
Ayyukan yan ta'adda ya yi kamari a yankin Arewa, inda aka sace mutane akalla 7,568 a cikin shekara daya kawai, kuma ana ci gaba da sata da kashe jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Fashi da makami, kwacen waya da garkuwa da mutane sun yi kamari a jihohin Kano, Kaduna da Zamfara, inda jama'a ke zaune cikin fargabar aukuwar daya da matsalolin uku.
Rahoton da Legit ta samu na nuna yadda mazauna wasu yankunan a jihohin su ke nuna cewa ba za su amince miyagu su ci gaba da yi masu hawan kawara ba.
A lokuta mabanbantan, an samu mutane su na afkawa miyagun har ta kai su yi nasarar kamawa ko kashe wasu daga cikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. An kama miyagu a Kano
A makon da ya gabata wasu yan daba su ka far wa mazauna Dorayi da ke karamar hukumar Kumbotso inda su ka yi sace-sacen waya da lalata kaya.
A nan ne jama'a su ka yi kukan kura, tare da lallasa hatsabibin dan daba, Abba Burakita, sannan aka mikawa yan sanda shi a galabaice, daga bisani ya rasu.
Mukhtar, wani mazaunin Kano ne, kuma ya shaidawa Legit cewa a hanyarsa ta komawa gida ya tarar yan daban su na kwace, dole ya sake hanya kafin jama'a su ka fusata.
2. Mazauna Zamfara sun fatattaki miyagu
Wasu mazauna garin Matusgi a karamar hukumar Talata Mafara, jihar Zamfara sun yi bajinta, inda su ka tunkari miyagun da su ka hana su sakat tare da sheke 37 daga cikinsu.
Lamarin ya afku ne bayan miyagun sun kutsa kauyen Matusgi, kamar yadda su ka saba shiga kauyuka a Zamfara da niyyar kwashe mutanen da za su yi garkuwa da su.
3. Yadda aka sheke miyagu a Kaduna
Su ma mazauna kauyen Rugar Sojidi a Kaduna sun fusata da yadda miyagu su ka raina su, tare da yi masu dauki dai-dai duk da babu laifin da su ka yi masu.
Bayan miyagun sun shiga kauyen inda su ka sace mutane uku, sai su ka sake dawowa domin su kara, lamarin da ya sa 'yan Rugar su ka mayar da martani har dan ta'adda daya ya mutu.
Sojoji za su dira kan miyagu
A baya kun ji cewa karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya ja tawagar hafsoshin tsaro zuwa Sakkwato bayan umarnin shugaba Bola Tinubu.
An gano Dr. Matawalle da babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa a yunkurin dawo da zaman lafiya yankin Arewa maso Yamma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng