Dalilin da Ya Sa ‘Yan Arewa Suka Mamaye Tawagar Tsaron Tinubu, Matawalle Ya Magantu

Dalilin da Ya Sa ‘Yan Arewa Suka Mamaye Tawagar Tsaron Tinubu, Matawalle Ya Magantu

  • Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya dage cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Arewa adalci wajen rabon mukaman gwamnati
  • Tsohon gwamnan na Zamfara ya ce shugaba Tinubu ya fahimci matsalar Arewa ta tsaro ce, shi ya sa ya nada 'yan Arewa a mukaman tsaro
  • Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da sojoji na runduna ta 8 da ke Sokoto a wani shiri na karfafa yaki da 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - A ranar Talata ne karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya dage kan cewa Shugaba Bola Tinubu ya yiwa Arewa adalci wajen nade-naden mukamai.

A cewar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Shugaban Tinubu ya cika manyan mukaman tsaro na gwamnatinsa da ’yan Arewa.

Kara karanta wannan

"A yi amfani da tsarin IBB": Janar Akilu ya ba Tinubu shawarar magance rashin tsaro

Matawalle ya kare Tinubu kan rabon mukamai
Matawalle ya zayyana muhimman mukaman da Tinubu ya ba 'yan Arewa. Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

A cewar Matawalle, Tinubu ya ba 'yan Arewa mukaman tsaro saboda ya na so a warware matsalar rashin zaman lafiya, musamman a yankin Arewa maso Yamma, inji Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya yi wa Arewa adalci" - Matawalle

Ministan ya yi wannan jawabi ne a Sokoto yayin wata ziyara da ya kai wa dakarun Operation Hadarin Daji a hedikwatar runduna ta 8 ta rundunar sojojin Najeriya da ke Sokoto.

Matawalle, wanda ya samu rakiyar babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce sun kai ziyarar ne bisa umarnin Shugaba Tinubu.

Ya ce shugaban kasar ne ya kira su daga kasar Sin, inda ya umarce su da su je Sokoto domin tattaunawa da sojojin domin duba matakan yaki da 'yan bindiga.

"Babu ko shakka matsalarmu ta tsaro ce, shi ya sa shugaban kasar ya nada tawagar tsaronsa daga Arewa, ciki har da ni kaina da kuma ministan tsaro."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga uku: Gwamnati ta ba hafsoshin tsaro umarnin tarewa a Sokoto

- Inji karamin ministan tsaro.

Masu mukaman tsaro daga Arewa

The Guardian ta ruwaito Matawalle ya ce shugaban kasa ya zabo 'yan Arewa ya ba su manyan mukaman tsaro da suka hada da karamin ministan tsaro (shi Matawalle) daga Zamfara.

Sauran sun hada da babban hafsan tsaro daga Kaduna, ministan tsaro daga Jigawa, mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro daga Adamnawa da ministan harkokin 'yan sanda daga Yobe.

Ministan ya kuma karfafi guiwar sojojin inda ya ce ka da su damu da abubuwan da suka faru a jihar, kamar kisan sojoji hudu da kuma kona motocin sulke na sojoji da tawagar Bello Turji ta yi.

ISWAP ta magantu kan harin Yobe

A wani labarin, mun ruwaito cewa kugiyar ta'addanci ta ISWAP ta dauki alhakin kai hari garin Mafa da ke jihar Yobe a ranar Lahadin da ta gabata.

A wata wasika da kungiyar ta fitar, ta ce ita ce ta kashe kimanin mutane 87 a harin da ta kai saboda wasu laifuffuka da ta ce 'yan garin sun yi mata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.